Yayin da Ake Fama a Najeriya, Gwamnan APC Ya Ware Biliyan 3.75 Don Siyan Turare da Fanka a Ofishinsa

Yayin da Ake Fama a Najeriya, Gwamnan APC Ya Ware Biliyan 3.75 Don Siyan Turare da Fanka a Ofishinsa

  • Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya sha suka bayan ware biliyan 3.75 son sauya turare da kuma fanka a gwamnatinsa
  • Sanwo-Olu ya ware miliyan 75 don sauya turare a ofishinsa yayin da aka ware biliyan uku a ofishin mataimakinsa don siyan fanka
  • Wannan na zuwa ne bayan cece-kuce da 'yan Najeriya su ka yi kan ware kudade da Majalisun Tarayya su ka yi na siyan motocin alfarma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - 'Yan Najeriya da dama sun soki Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas kan ware makudan kudade don siyan turare da fanka a gwamnatinsa.

Sanwo-Olu ya ware miliyan 7.5 don sauya turaren da ke ofishinsa da kuma biliyan uku na siyan fanka a ofishin mataimakinsa, Hamzat Obafemi.

Kara karanta wannan

Hadiman 'yan majalisar dokokin Najeriya sun koka kan rashin biyansu albashin watanni 15

Cece-kuce yayin Gwamna Sanwo-Olu ya kashe biliyoyin kudade don siyan turare da fanka
Gwamna Sanwo-Olu na Legas ya kashe biliyan 3.75 kan siyan turare da fanka. Hoto: Babajide Sanwo-Olu.
Asali: Getty Images

Nawa Sanwo-Olu ya ware na kudaden?

Sauran sun hada da ware miliyan 440 na siyan motocin alfarma a ofishin shugaban ma'a'ikatansa, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, ofishin ya samu amincewar miliyan 18 don samar da kaji dubu biyu ga kananan hukumomi da ke jihar da unguwanni.

Gwamnan ya kuma ware miliyan 152 don gyaran ruwa a fadar mai martaba Oba na Legas, Legit ta tattaro.

Mene 'yan Najeriya ke cewa kan siyan motocin Majalisa?

Wannan na zuwa makwanni kadan bayan ware miliyoyin kudade da Majalisun Tarayya su ka yi na siyan sabbin motocin alfarma.

Hakan ya jawo kace-nace a tsakanin al'umma inda aka soki shirin nasu ganin irin halin da kasar ke ciki.

Daga bisani Majalisar ta kare kanta da cewa sun yi hakan ne don samun motoci ma su karfi da za su dade su na amfani da su.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Tsohon kwamishinan 'yan sanda a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya, Sifeta ya kadu

Har ila yau, sun yi korafin cewa 'yan kasar sun saka wa Majalisar ido yayin da akwai ministoci da ke da motocin alfarma amma ba a magana.

Tinubu ya karyata siyan jirgin ruwan alfarma

A wani labarin, Shugaba Tinubu ya karyata jita-jitar cewa ya bukaci siyan jirgin ruwan alfarma don bukatarsa.

Tinubu ya ce an riga an biya kudaden tun a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Wannan na zuwa ne bayan 'yan Najeriya sun yi ta korafin cewa Tinubu na wasa da dukiyar al'ummar kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.