Sojoji Sun Yi Wa Kwamandan Boko Haram Ruwan Bama-Bamai a Mabuyarsa Da Ke Kaduna
- Sojojin saman Najeriya sun samu nasarar kai wasu farmake-farmake kan wani kwamandan Boko Haram da dan uwansa da suka addabi jihar Kaduna da Niger
- Rundunar sojin ta kai hare-haren ne bayan samun wasu rahotannnin sirri na cewa dan ta'addan mai suna Boderi da mambobinsa na zaune a Tsauni Doka
- Boderi da dan uwansa, na da alhaki a kai hare-hare da dama a kan al’umomin jihar Kaduna da kewaye
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kaduna - An kashe ‘yan ta’adda da dama a wani samame da rundunar sojin sama ta Operation Whirl Punch ta kai a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.
Sojojin sun kai harin ne bayan wani rahoton sirri da rundunar ta samu na cewa wani dan ta'adda mai suna Boderi da mambobinsa sun yi mafaka a wurin, jaridar Punch ta ruwaito.
Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar sojin saman Najeriya Air Commodore Edward Gabkwet ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata, shafin Nigeria Air Force ya ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda rundunar sojin sama ta tarwatsa mabuyar Boderi
Air Commodore Gabkwet ya ce rundunar ta samu nasarar a harin da ta kai sansanin ta hanyar yin ruwan bama-bamai ta jiragen sama, lamarin da ya sa hukumar ta sake kai wani samame a mabuyar dan uwan Boderi.
Nigeria Bulletin ta ruwaito Gabkwet na cewa ‘yan uwan biyu na da alhaki a kai hare-hare da dama a kan al’umomin jihar Kaduna da kewaye,
Ya ce,
“Rundunar sojin saman Najeriya karkashin Operation Whirl Punch ta ci gaba da kai hare-hare ta sama kan ‘yan ta’addan da ke aiki a shiyyar Arewa maso Yamma da Arewa ta tsakiya.
Nasara: Dakarun sojoji sun kai samame maɓoyar 'yan bindiga akalla 5 a Arewa, sun samu gagarumar nasara
"Hare-haren sun kai ga halaka wasu ‘yan ta’adda a Tsauni Doka da ke karamar hukumar Igabi a Kaduna. "
“Harin ya zama dole ne biyo bayan bayanan sirri da aka samu da suka nuna akwai wani shugaban ‘yan ta’adda da aka fi sani da Boderi da dakarun sa da suka yi mafaka a Tsauni Doka."
Laifukan da ake zargin Boderi da mayakan sa sun aikata - NAF
Kakakin rundunar sojin, ya kuma kara da cewa:
"An kuma kai hari makamancin wannan a wani wuri mai tazarar mita 500 gabas da maboyar Boderi, inda ake kyautata zaton mabuyar dan uwan Boderi, Nasiru ne."
“An zargi Boderi da dan uwansa, Nasiru, tare da ‘yan kungiyarsu da wasu hare-hare da sace-sace da aka yi a hanyar Abuja zuwa Kaduna, Kaduna zuwa Birnin Gwari da kuma wasu garuruwan jihohin Neja da Kaduna. "
NDLEA ta sake kama hatsabibin dilallin kwayoyi a Abuja
Rundunar NDLEA ta samu nasarar sake kama wani dillalin kwayoyi mai suna Ibrahim Momoh wanda ya tsere daga gidan yari a Abuja shekaru bakwai da suka gabata, Legit Hausa ta ruwaito.
Asali: Legit.ng