Adadin Wadanda Suka Mutu a Gaza Ya Haura 13,000, Inji Gwamnatin Hamas
- Akalla mutane 13,000 ne suka mutu sakamakon farmakin da Isra'ila ke ci gaba da kai wa kan mazauna zirin Gaza tun watan Oktoba
- Yaki ya barke tsakanin dakarun Hamas da kuma sojojin Isra'ila kan farmakin da Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata
- Yaki tsakanin Isra'ilawa da mutanen Falasdinu ba sabo bane, hakan ya faro ne tun bayan mamayar Isra'ila a yankin Larabawa
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
Zirin Gaza - Gwamnatin Hamas ta ta ce ya zuwa yau Lahadi adadin mutanen da suka mutu sakamakon fadan da ake gwabzawa tsakanin sojojin Isra'ila da mayakan Hamas a yankin Falasdinu ya kai 13,000.
Rikici tsakanin Isra'ila da Hamas ya fara ne tun ranar 7 ga watan Oktoba., inda mayakan Hamas suka farmaki mazauna Isra'ila, Channels Tv ta ruwaito.
Bayan haka ne gwamnatin Isra'ila ta fara kai harin daukar fansa kan mazauna Gaza a nufin lallasa dakarun Hamas da ke boye a ramukan kariya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutanen da aka akshe a Gaza
Gwamnatin Hamas ta ce sama da 5,500 ne yara daga cikin wadanda suka mutu, tare da mata 3,500, inda aka jikkata wasu mutane 30,000, India Times ta tattaro.
A baya ma’aikatar lafiya ta kasar ta ce ba za ta iya bayar da adadin adadin wadanda aka kashe ba saboda yadda aka danne gawarwaki da yawa a kasan baraguzan gine-gine.
An fara yakin Gaza da Isra'ila ne shekaru da dama, wanda hakan ya cinye rayukan mutane da yawa, musamman Falasdinawa.
An yi zabe kan tsagaita wuta a Gaza
A wani labarin, Najeriya da wasu kasashe 119 ne a ranar Juma'a suka kada kuri'ar amincewa da kudurin da ke kira da a samar da "zaman lafiya mai dorewa" tsakanin sojojin Isra'ila da Hamas a Gaza.
Har ila yau, tanasun amince da ci gaba da shigar da kayayyakin agaji da rayuwar yau da kullum a yankin na Zirin Gaza mai fama da takurar Isra'ila, rahoton Al-Jazeera.
Kudirin da kasashen Larabawa suka shirya ya samu kuri'u 120 na goyon baya, 14 na adawa da kuma 45 suka ki bayyana matsayarsu.
Asali: Legit.ng