Jerin Manyan Motocin Karau da Ake Zargin Tsohon Gwamnan CBN Emefiele Ya Siya da N1.2bn Na Kudin Kasa
- Godwin Emefiele, tsohon gwamnan babban bankin kasa (CBN), ya gurfana a gaban kotu bisa wasu tuhume-tuhume shida
- Gwamnatin tarayya ta hannun EFCC ta shigar da Emefiele kara tare da tuhumarsa da abubuwa guda 20, amma daga baya aka mayar da su zuwa shida
- Ana tuhumarsa ne da kashe wasu kudaden da suka kai Naira biliyan 1.6, wanda aka ce ya yi amfani da su wajen siyan manyan motocin karau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta gurfanar da tsohon gwamnan babban bankin kasa (CBN) Godwin Emefiele bisa zarginsa da wasu tuhume-tuhume gida shiga.
A tun farko, an shigar da karar ne tare da tuhume-tuhume 20 da suka hada da kudi Naira biliyan 6.5, wadanda daga baya aka rage su zuwa shida da kudi Naira biliyan 1.6, Legit ta tattaro.
A ranar Juma’a ne tsohon gwamnan na CBN ya gurfana gaban kotu domin neman beli, inda ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa bayan an karanta masa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka sake kama Emefiele
Bayan hukumar DSS ta sake shi, nan take Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta sake kama shi a ranar 27 ga watan Oktoba, sannan gwamnatin tarayya ta gyara tuhume-tuhumen da ake yi masa.
A cewar takardar karar, har yanzu dai tuhume-tuhumen suna nan ne a kan zargin sayen kayayyaki da kudaden gwamnati.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana zargin cewa, Emefiele ya sayi motocin karau guda 43 ba bisa ka’ida ba tsakanin shekarar 2018 zuwa 2020 na Naira biliyan 1.2.
Motocin da ake zargin ya siya
- Motocin Toyota Hilux guda 37: N854.7m
- Mota Toyota Avalon guda 1: N99.9m
- Mota Toyota Landcruiser V8 guda 1: N73.8m
- Motoci Toyota Hilux Shell guda 2: N44.2m
- Motoci Toyota Landcruiser VXR V8 guda 2: N138m
An ba Emefiele masauki a gidan yari
A tun farko, Babban Kotun Tarayya ta umarci a tsare tsohon gwamnan babban bankin kasa a shari'ar da ake masa na rashawa.
Jim kadan bayan hawan shugaba Tinubu, aka kame Emefiele tare da tsare bisa zargin kawo cikas ga lamurran kasa.
Asali: Legit.ng