Gwamnatin Tinubu Ta Bude Shafin Intanet Domin Rajistar Daukar Aiki? Gaskiya Ta Bayyana
- Adadin marasa aikin yi a Najeriya ya kai kaso 33.3% bisa 100, kamar yadda hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta nuna
- Ma'anar wannan ita ce, fiye da mutane miliyan 23 ko dai ba su da aiki ko suna aiki na ƙasa da da sa'o'i 20 a mako
- Yawan marasa aikin yi da ke neman ayyukan yi ya sa ake yawan samun ƴan damfara, amma wani rahoton bincike na gaskiya ya gargaɗi mutane da kada su faɗa ga ƴan damfara
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Wasu rubuce-rubucen kafafen sada zumunta da dama sun yi iƙirarin cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta buɗe shafin yanar gizo da za ta yi rajistar waɗanda za su ci gajiyar wani sabon shiri na yin aiki domin samun kuɗi.
Adadin marasa aikin yi a Najeriya ya kai kaso 33.3% cikin 100 a cikin Q4 na shekarar 2020. Sai dai a baya-bayan nan Hukumar Ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta bayyana rashin aikin yi da kaso 5.3% bisa 100 (Q4 2022) da kaso 4.1% (Q1 2023), bisa la’akari da sabon binciken hukumar NLFS.
Kanun labarin da wani shafin Facebook ya sanya yana cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Shirin samar da ayyukan yi na sabunta fata (RHJCP) 2023: Yadda ake nema a kyauta."
An kuma samu saƙon a nan, nan, da nan.
Kanun labarai yana haɗe zuwa labarin wani shafin yanar gizo game da shirin samar da aikin yi.
Amma a daidai lokacin da masu niyya suka shiga, sai a gaya musu cewa ba a fara nema ba.
Rubutun na cewa:
"A halin yanzu, ba a fara karɓar buƙatar masu nema ba, saboda ana cigaba da haɓaka shafin yanar gizon."
"Da zarar an kammala, za mu samar muku da hanyar shiga shafin yanar gizon. Ku cigaba da sa ido kan voiceofnigeria.org.ng domin samun ƙarin bayani."
Amma shin gaskiya ne? Dandalin binciken gaskiya, Africa Check, ya yi bincike.
Hattara da ƴan zamba
Africa Check ta ce babu daya daga cikin hanyoyin da ke cikin labarin da ya kai ga wurin da za a yi rajista. Dandalin ya ce "duk wajen labarin ɗaya su ke komawa."
"Wannan yaudara ce irin ta ƴan zamba."
Za a Fara Biyan Bashin N-Power
A wani labarin kuma, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta shirya fara biyan basussukan da ma'aikatan N-Power suka biyo ta na wata da watanni.
Gwamnatin tarayyar ta yi bayanin cewa za a fara biyan albashin ma'aikatan da ya maƙale a cikin watan Nuwamban 2023.
Asali: Legit.ng