'Yan Bindiga Sun Halaka Babban Malamin Addini da Yin Awon Gaba da Matarsa a Wani Sabon Hari

'Yan Bindiga Sun Halaka Babban Malamin Addini da Yin Awon Gaba da Matarsa a Wani Sabon Hari

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun salwantar da ran wani fasto na cocin Evangelical Church Winning All (ECWA) a jihar Kaduna
  • Ƴan bindigan a yayin harin da suka kai sun yi awon gaba da matar faston bayan sun farmaki ƙauyen na Damakasuwa
  • Al'ummar yankin sun buƙaci gwamnati da hukumomin tsaro su taimaka wajen ceto matar wacce ke hannun ƴan bindigan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kashe wani Fasto mai suna Amako Maraya, mai kula da cocin Evangelical Church Winning All (ECWA) da ke Damakasuwa a ƙaramar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.

Miyagun ƴan bindigan bayan sun halaka faston sun kuma yi awon gaba da matarsa, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Mutum 1 ya rasu yayin da matasa suka yi fito na fito da 'yan bindiga bayan sun yi yunkurin kai hari

'Yan bindiga sun halaka fasto a Kaduna
'Yan bindiga sun halaka babban fasto a Kaduna Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Wani mazaunin ƙauyen, wanda kuma dattijo ne a cocin, Mista Ishaku Chinge, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Asabar, ya ce ƴan bindigan sun farmaki ƙauyen ne da misalin karfe 11:00 na daren ranar Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ƙara da cewa kimanin watanni uku da suka gabata ƴan bindigan sun yi yunƙurin yin garkuwa da ɗan faston, amma da taimakon jama'a an kore su, duk da cewa yaron ya samu rauni, rahoton Daily Post ya tabbatar.

A kalamansa:

"A ranar Juma'a ma sun kai farmaki gidansa inda suka yi bindige shi tare da yin garkuwa da matarsa."
"Ƴan bindigan sun kira waya da safe, inda suka buƙaci iyalansa su a biya su Naira miliyan uku. Ba su sake kira ba."

Ana zaman ɗar-ɗar a yankin

A cewarsa, tun bayan aukuwar lamarin, ana ta zaman ɗar-ɗar a tsakanin al’ummar yankin.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun cafke wani tantirin mai ba yan ta'addan ISWAP bayanai a Borno

Ya ƙara da yin kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su taimaka wajen ceto matar wacce ke cikin wani mawuyacin hali a yanzu.

Muƙaddashin jami'in hulɗa da jama'a na ƴan sandan jihar Kaduna, Mansir Hassan, bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ta waya ba har ya lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Ƴan Bindiga Sun Halaka Malamin Addini

A wani labarin kuma, wasu miyagun ƴan bindiga sun halaka wani babban fasto bayan sun karɓi kuɗin fansa a jihar Kogi.

Ƴan bindigan dai sun sace faston ne sannan bayan sun karɓi kuɗin fansa har N1m daga hannun iyalansa suka halaka shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng