Abba Gida-Gida Ya Magantu Bayan Kotun Daukaka Kara Ta Tsige Shi Daga Kujerar Gwamnan Kano

Abba Gida-Gida Ya Magantu Bayan Kotun Daukaka Kara Ta Tsige Shi Daga Kujerar Gwamnan Kano

  • Gwamnan mai ci a jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke matsayin "rashin adalci ga al'umar Kano"
  • Gwamna Yusuf, ya ce da shi da jam'iyyar sa, sun shirya shigar da sabuwar kara a Kotun Koli, inda suke da yakinin za a kwatar masu hakkin su
  • A ranar Juma'a ne Kotun Daukaka Kara ta kori Abba daga gwamnan Kano, tare da tabbatar da Nasiru Gawuna matsayin halastaccen gwamnan jihar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce Kotun Daukaka Kara ba ta yi wa al'ummar jihar Kano da jam'iyyar NNPP adalci a hukuncin da ta yanke ba.

Kara karanta wannan

Shari'ar Gwamnan Kano: NNPP ta bayyana matsayarta kan hukuncin Kotun Koli tare da matakin na gaba

Gwamnan, wanda ya bayyana hakan a yayin zanta wa da manema labarai, ya kuma ce lauyoyin su za su shigar da sabuwar kara a Kotun Koli ta Najeriya.

Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba ya ce hukuncin kotun ba zai hana su ci gaba da yin ayyukan raya al'umar a jihar Kano ba Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Kotun Daukaka Kara ta kori karar Abba Kabir Yusuf

A ranar Juma'a, 17 ga watan Nuwamba, Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da hukuncin da kotun kararrakin zabe ta yanke na korar Abba Kabir daga kujerar gwamna, Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ta kuma ayyana Nasiru Gawuna matsayin zababben gwamnan jihar Kano, bisa dalilai da suka hada da soke wasu kuri'u na Abba, da kuma kasancewar Abba ba mamba ba ne a jam'iyyar NNPP.

Sai dai gwamnan Kanon, ya ce da shi da jam'iyyar sa sun cimma matsaya na shigar da wata sabuwar kara a Kotun Koli, inda suke sa ran za a kwatar masu hakkin su, kamar yadda BBC Hausa ta wallafa bidiyon hirar.

Kara karanta wannan

Kano: Wane hali ake ciki a birnin bayan kwace kujerar Abba Kabir da kotun daukaka kara ta yi?

Muna da yakinin Kotun Koli za ta kwatar mana hakkin mu - Abba Kabir

Yusuf ya ce:

"Muna da yakinin cewa Kotun Koli za ta kwato mana hakkinmu, akan wancan rashin adalci da aka yi mana baki daya"
"Kuma ina kira ga al'ummar Kano, da su ci gaba da kasuwancin su da dukkan abubuwa na walwala, domin mun yi magana da jami'an tsaro, wajen kare rayukan su da dukiyoyin su"

Gwamnan ya ci gaba da cewa:

"Muna so al'ummar jihar Kano su san cewa, wannan matsala da ta faru, na dan wani lokaci, sannan muna fatan in Allah ya yarda, Kotun Koli za ta karbo maku hakkin ku."
"Kuma muna yi maku alkawari, wannan abin da ya faru ba zai tsoratar da mu ko saka mu ja da baya daga ayyukan raya al'umma da mu ke yi ba."

Shari'ar gwamnan Kano: NNPP ta garzaya Kotun Koli

A wani labarin makamancin wannan; jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ta bayyana bakin cikinta game da hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke, da ta kori gwamnan Kano, Abba Yusuf.

Jam'iyyar ta ce za ta binciki duk wata hanya ta doka da za ta kwato mata hakkinta, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel