Innalillahi: Jirgi Ya Gamu da Mummunan Hatsari a Jihar Arewa, Mutane da Yawa Sun Mutu

Innalillahi: Jirgi Ya Gamu da Mummunan Hatsari a Jihar Arewa, Mutane da Yawa Sun Mutu

  • Mummunan hatsarin jirgin ruwa ya yi ajalin mutane 10 a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja
  • Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar (NSEMA) ce ta tabbatar da haka, ta ce Kwale-Kwalen na ɗauki mutum 34 lokacin da haɗarin ya afku
  • Ta bayyana cewa shugaban ƙaramar hukumar Shiroro da babban jami'in hukumar sun ziyarci wurin da hatsarin ya afku

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - Rahotanani sun nuna aƙalla mutum 10 ne suka rasu a wani sabon hatsarin jirgin ruwa da ya afku a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Hadarin jirgin ruwa a jihar Neja.
Tashin Hankali Yayin da Sabon Hatsarin Jirgi Ya Lakume Mutane 10 a Jihar Niger Hoto: pmnews

Shugaban sashin kai agaji na hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja (NSEMA), Alhaji Garba Salihu, ne ya bayyana haka a Minna, babban birnin jihar ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan

Mummunan hatsarin mota a Kano ya yi sanadin salwantar rayuka 4 da jikkata wasu da dama

Ya ce hukumar ta samu rahoton wani hatsarin kwale-kwale a yankin karamar hukumar Shiroro wanda ya afku a ranar 16 ga watan Nuwamba da misalin karfe 2:00 na rana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane da yawa sun tsallake rijiya da baya

Salihu ya ce kimanin fasinjoji 34 ne ke cikin jirgin ruwan, waɗanda suka haɗa da maza 20 da mata 14, kamar yadda jaridar PM News Nigeria ta ruwaito.

Ya ce an kubutar da mutane 24 da suka tsira da rayuwarsu, tare da gano gawar mutum daya, ya kara da cewa ana ci gaba da aikin ceto sauran mutanen da suka bata.

Ya ce wadanda suka rasu a haɗarin sun hada da Farida Muntari, Sharhabila Sagir, Abubakar Sadiq, Na’ima Ibrahim, Amina, Safaratu Ibrahim, Sadiq Ibrahim, Rafiya Yakubu da gawarwaki biyu da ba a tantance ba.

Menene ya haddasa hatsarin jirgin?

Kara karanta wannan

Nasara: Dakarun sojoji sun kai samame maɓoyar 'yan bindiga akalla 5 a Arewa, sun samu gagarumar nasara

A cewarsa, jirgin ruwan na da direbobi shida da suka hada da Dahiru Yusuf, Sa’idu Shu’aibu, Ahmadu Garba, Sa’idu Garba, Abdulaziz Yahaya, da Lukuman Sani.

Salihu ya kara da cewa hatsarin kwale-kwalen ya faru ne sanadin boren ruwa, da igiyar ruwa mai karfi, da kuma wata bishiya, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Bayan haka kuma Salihu ya bayyana cewa shugaban karamar hukumar Shiroro tare da jami’in kula da ofishin hukumar sun ziyarci wurin da lamarin ya faru.

Legit Hausa ta samu zantawa da wani mazaunin ƙaramar hukumar Shiroro, jihar Neja, wanda hatsarin ya rutsa da matar abokinsa.

Mutumin mai suna, Habib Sa'idu, ya shaida wa wakilinmu cewa an samu nasarar ciro gawar mutum tara, saura ɗaya ya rage ana nema.

Ya ce:

"Eh tabbas jirgin ruwa ya yi hatsari kuma harda matar abokina a ciki, suna da yawa fasinjojin amma 10 ne suka mutu, an ciro gawar mutum tara saura ɗaya ake nema."

Kara karanta wannan

Gwamnatin jihar Kaduna za ta birne gawarwakin mutane 60

Yan Bindiga Sun Halaka Dakaraun Yan Sanda

A wani rahoton kuma Wasu yan bindiga da ake zargin mayakan ESN ne sun yi ajalin yan sanda biyu a gefen birnin Abakaliki da ke jihar Ebonyi.

Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce sauran waɗanda suka ji rauni na asibiti ana musu magani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262