Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Kan Jami'an Tsaro, Sun Kashe Wasu Tare da Tafka Mummunar Ɓarna
- Wasu yan bindiga da ake zargin mayakan ESN ne sun yi ajalin yan sanda biyu a gefen birnin Abakaliki da ke jihar Ebonyi
- Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce sauran waɗanda suka ji rauni na asibiti ana musu magani
- Ta kuma bayyana cewa jami'an yan sanda na kokarin zakulo maharn duk inda suka shiga, ta nemi jama'a su taimaka da bayanan sirri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ebonyi - Rundunar ƴan sanda reshen jihar Ebonyi ta tabbatar cewa wasu 'yan ta'adda sun halaka yan sanda biyu yayin da suka fita sintiri a titin Nwofe a birnin Abakaliki, jihar Ebonyi.
Yan bindigan waɗanda ake zaton mayaƙan haramtacciyar ƙungiyar yan aware (IPOB) da mayaƙanta ESN ne sun faramaki yan sanda a wata motar Highlander mara lamba.
Nasara: Dakarun sojoji sun kai samame maɓoyar 'yan bindiga akalla 5 a Arewa, sun samu gagarumar nasara
Jaridar Leadership ta rahoto cewa hakan na ƙunshe a wata sanarwa da jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar yan sandan Ebonyi, SP Onome Onovwakpoyeya, ta fitar ranar Jumu'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta bayyana cewa maharan sun bindige jami'an yan sandan biyu har lahira yayin da sauran suka jikkata kuma suna kwance a asibiti ana musu magani.
Kakakin ƴan sandan ta bayyana cewa kwammishinar ƴan sandan jihar, CP Augustina Ogbodo, ta samu rahoton harin kuma nan take ta tura ƙarin dakaru zuwa wurin.
Wane mataki hukumar ƴan sanda ta ɗauka?
A cewarta, ba tare da ɓata lokaci ba dakarun yan sandan suka kai ɗauki inda suka nuna wa yan ta'addan kwarewar aiki amma abin baƙin cikin dukkan maharan suka tsira.
“Kwamishinan ‘yan sandan ta ziyarci wurin da lamarin ya faru tare da manyan jami’ai domin gani da ido da kuma tantancewa."
SP Onovwakpoyeya ta kara ce CP ta yi kira ga masu kishin jihar da su baiwa rundunar bayanai masu amfani da za su taimaka wajen kama maharan da suka gudu, Punch ta ruwaito.
Dakarun Sojoji Sun Kai Samame Maboyar Yan Bindiga
A wani rahoton na daban Gwarazan sojojin Najeriya sun sake kai samame kan maɓoyar ƴan bindiga a yankuna da dama a jihar Zamfara.
Kakakin rundunar Operation Hadarin Daji, Kaftin Yahaya Ibrahim, ya ce sojojin sun halaka yan bindiga sun kwato mutum 5.
Asali: Legit.ng