Nasara: Dakarun Sojoji Sun Kai Samame Maboyar Yan Bindiga 5 a Arewa, Sun Samu Gagarumar Nasara

Nasara: Dakarun Sojoji Sun Kai Samame Maboyar Yan Bindiga 5 a Arewa, Sun Samu Gagarumar Nasara

  • Gwarazan sojojin Najeriya sun sake kai samame kan maɓoyar ƴan bindiga a yankuna da dama a jihar Zamfara
  • Kakakin rundunar Operation Hadarin Daji, Kaftin Yahaya Ibrahim, ya ce sojojin sun halaka yan bindiga sun kwato mutum 5
  • A cewarsa, ƙarfin luguden wuta da jajircewar dakarun sojin ne suka tilastawa yan ta'addan tserewa bisa tilas ɗauke da raunuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Dakarun sojojin rundunar Operation Hadarin Daji da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a Arewa maso Yamma sun halaka yan bindiga a Zamfara.

Sojoji sun samu nasara kan yan bindiga.
Sojoji Sun Murkushe Yan Bindiga, Sun Ceto Mutane Biyar da Aka Sace a Zamfara Hoto: channelstv
Asali: UGC

A wani samamen shara da suka kai kan yan ta'addan, dakarun sojin sun ragargaji yan bindigan tare da ceto mutane 5 da aka yi garkuwa da su a jihar.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta rasa ɗan Majalisa ɗaya tilo da take da shi a jihar Arewa, ya koma APC

Mai magana da yawun rundunar Operation Hadarin Daji, Kaftin Yahaya Ibrahim, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Jumu'a, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, sojojin sun kai samamen haɗin guiwa kan maɓoyar ƴan bindigan a yankuna da dama na jihar Zamfara ranar 16 ga watan Nuwamba, 2023.

Garuruwan da sojojin suka kai wannan farmaki kan ƴan ta'addan sun haɗa da Tugan Gama, Tugan Hausawa, Tugan Nabaru, Yarsabia da Daji Yanayin Kari a ƙaramar hukumar Anka.

Ibrahim ya bayyana cewa yayin haka ne sojojin suka ci karo tare da sheƙe yan ta'addan biyu, sauran kuma suka ari na kare ɗauke da raunukan harbin bindiga.

Sojoji sun daƙile mummunan hari. yan bindiga

Bayan haka kuma jami'an sojin sun kai ɗaukin gaggawa yayin da suka samu kiran cewa yan fashin daji sun kai farmaki ƙauyen Yarkoria da ke yankin Anka a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Hatsabiban ƴan bindiga sun gamu da ajalinsu yayin da suka kai hari a jihar arewa, su duka sun mutu

Ya ce ƙarfin luguden wutan sojojin ne ya tilasta wa maharan guduwa ba arziƙi suka bar mutanen da suka yi garkuwa da su, in ji rahoton The Cable.

“An yi nasarar ceto mutane biyar da suka hada da ƙaramin yaro, mata 2 da maza 3 kuma tuni suka sake komawa cikin iyalansu," in ji shi.

Jami'an Tsaro Sun Ɗauki Mataki a Wasu Wurare a Kano

A wani labarin Jami'an tsaro sun mamaye muhimman wurare ranar Jumu'a a cikin kwaryar birnin Kano domin daƙile duk wani yunƙurin tada yamutsi da karya doka da oda.

Dakarun tsaron sun ɗauki wannan matakin ne biyo bayan hukuncin da Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke na tsige Abba Kabir Yusuf daga matsayin gwamnan Kano .

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262