Alkali Ya Umurci a Bai Wa Emefiele Masauki a Gidan Yarin Kuje
- Kotu a Abuja ta bada sabon umurni game da bukatar neman beli na Godwin Emefiele
- Tsohon shugaban CBN din da ke fuskantar tuhuma zai kasance a gidan yari har zuwa ranar 22 ga watan Disamban 2023, lokacin da kotu za ta yanke hukunci kan bukatarsa na neman beli
- Hakan na kunshe cikin hukuncin da Mai Shari'a Hamza Muazu na Babban Kotun Tarayya a Abuja ya yanke a ranar Juma'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe
FCT, Abuja - Babban Kotun Tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja a Maitama, ta umurci a tsare tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele a gidan gyaran hali na Kuje kafin ya cika ka'idar belinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai Shari'a Hamza ne ya bada umurnin a ranar Juma'a bayan gurfanar da Emefiele tare da musanta aikata laifuka shida da Hukumar EFCC ke tuhumarsa a karar da ta yi wa kwaskwarima.
Abin da ya sa kotu ta mayar da Emefiele gidan yari?
A karar, an zarge shi da amfani da ofishinsa ta hanyar da ba ta dace ba da wasu abubuwan daban, rahoton The Nation.
Mai Shari'a Mu'azu, wanda ya saurari bukatar neman beli da Emefiele ya gabatar, ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 22 ga watan Nuwamba don yanke hukunci kan neman belin sannan a fara shari'a ranar 28 ga watan Nuwamba, rahoton The Cable.
FG ta rage tuhumar da ta ke yi wa Emefiele
A baya, Legit ta rahoto cewa gwamnatin tarayya ta rage yawan tuhume-tuhumen damfara da ta shigar kan tsohon gwamnan na Babban Bankin Najeriya.
Gwamnatin tarayya ta rage tuhume-tuhumen, wanda da farko 20 ne amma yanzu sun dawo shida. Tuhumar na da alaka da zargin siyo wasu kayayyaki.
Dakaci karin bayani ...
Asali: Legit.ng