“Ban Taba Busa Sigari Ko Shan Giya Ba”, Akpabio Ya Fadawa Daliban Najeriya

“Ban Taba Busa Sigari Ko Shan Giya Ba”, Akpabio Ya Fadawa Daliban Najeriya

  • Shugaban majalisar dattawan Najeriya, kuma lamba uku a kasar, Godswill Akpabio, ya shaida wa duniya cewa bai taba shan sigari ko barasa ba
  • Akpabio ya ce tun daga yarintarsa har zuwa girma, yana kiyaye tarbiyar da iyayensa suka basa, kuma yana kiyaye burikansa na rayuwa
  • Lamba ukun, ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi ga dalibai daga makarantun sakandare daban-daban na fadin kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce bai taba shan taba sigari ko kuma kurbar barasa ba, tsawon rayuwarsa.

Akpabio ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Abuja, yayin da yake jawabi ga dalibai daga makarantun sakandare daban-daban na fadin kasar.

Kara karanta wannan

2027: Atiku ya fara kiran Obi, Kwankwaso da sauran jam’iyyun adawa su hada-kai

Godswill Akpabio
Akpabio ya ce, ya kamata dalibai su kauracewa shan sigari ko kuma kurbar barasa. Hoto: Godswill Akpabio
Asali: Facebook

Makarantun sun halarci gasar kacici-kacici ta kasa da cibiyar nazarin dokoki da dimokuradiyya (NILDS) ta shirya mai taken: ‘doka da dimokuradiyya’.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har gobe ina kiyaye tarbiyar da iyaye na suka ba ni - Akpabio

Shugaban majalisar dattawan ya ce, ya kamata daliban su yi kokarin zama shuwagabanni masu hangen nesa ta hanyar kauracewa dabi’un da ka iya shafar burinsu na rayuwa, a cewar rahoton The Cable.

Akpabio, ya ce:

“A nawa bangaren, ban taba shan sigari ko shan barasa ba. Saboda har na girma, ina sauraron shawarwari da kiyaye tarbiyar da iyayena suka ba ni."
“Sa’ad da nake yaro, na kan ga wani mutum yana yin tangadi a hanya, kuma har ya faɗa cikin magudanar ruwa. Na tambayi mahaifiyata dalilin haka, ta sanar da ni hakan ya faru da shi ne don ya sha giya ya bugu."

Kara karanta wannan

NLC Ta Rubutawa Ma’aikatan Wuta, Makarantu Takardar Dunguma Yajin Aiki a Najeriya

A nasa bangaren, Abubakar Sulaiman, babban daraktan hukumar NILDS, ya ce makarantu masu zaman kansu da na gwamnati ne suka halarci gasar saboda kudurin majalisar dokokin kasar na ba da fifiko kan ilimi, Daily Trust ta ruwaito.

Akpabio Ya Tura Muhimmin Sako Ga Tinubu

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya bukaci Shugaba Tinubu ya kori ma su mukamai da ke bijirewa umarnin Majalisar, Legit Hausa ta ruwaito.

Akpabio na magana ne kan ma su rike da madafun iko da ke kin amsa gayyatar Majalisar don karin bayani ko wani abu makamancin haka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.