Yan Sanda Sun Yi Harbi Don Tarwatsa Masu Zanga-Zangan Goyon Bayan Falasdinu a Kaduna

Yan Sanda Sun Yi Harbi Don Tarwatsa Masu Zanga-Zangan Goyon Bayan Falasdinu a Kaduna

  • Yan sanda sun tarwatsa yan kungiyar Shi’a da ke zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa
  • Masu zanga-zangar goyon bayan yan Gaza wadanda kasar Isra’ila ke yi wa luguden wuta
  • Jami'an yan sanda sun harba barkonon tsohuwa tare da yin harbi a sama don tarwatsa masu zanga-zangar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Kaduna - Rundunar yan sanda a jihar Kaduna ta tarwatsa wani zanga-zangar goyon bayan Falasdinu da mambobin kungiyar yan uwa Musulmai na Shi'a suka shirya.

Masu zanga-zangar suna nuna goyon bayansu ne ga mutanen Gaza a Falasdinu wadanda Isra'ila ke yi wa yayyafin wuta tun a ranar 7 ga watan Oktoba, rahoton Daily Trust.

Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu
Yan Sanda Sun Yi Harbi Don Tarwatsa Masu Zanga-Zangan Goyon Bayan Falasdinu a Kaduna Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Yan shi'an, wadanda suka fara zanga-zangarsu daga harabar ofishin Kungiyar Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) da ke jihar Kaduna, sun yi tattaki ta hanyar Muhammadu Buhari Way zuwa ofishin hukumar kare hakkin dan adam na kasa don mika takardar kokensu.

Kara karanta wannan

Yan bindigar da suka sace ma'aikacin CBN da wasu 2 suna neman N10m kudin fansa

Yan mintoci da fara zanga-zangar, sai jami'an rundunar yan sandan Najeriya suka harba barkonon tsohuwa tare da harbi a sama don tarwatsa masu zanga-zangar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rayuka biyu sun salwanta a harin

Wasu rahotanni da ba a tabbatar ba sun nuna cewa an kashe mutane biyu a zanga-zangar, rahoton Aminiya.

Aliyu Umar Tirmizi, wanda ya yi jawabi a madadin masu zanga-zangar ya ce:

"Tun kusan kwanaki 75 kenan da yahudawan Isra'ila aiwatar da kisan kare-dangi da wariyar launin fata a kan fararen hular da ba su ji ba, ba su gani ba, cikinsu har da maza, mata da ma kananan yara.
"Sun murkushe dubban yara da tsofaffi sannan sun ruguza gidaje da wuraren bauta na bayin Allah yan farar hula. Wadannan Yahudawan Isra'ila sun keta haddin masallacin birnin Kudus, sannan suna yi wa bayin Allah da suka je bauta a wajen ta'asa.

Kara karanta wannan

Wasu sun sace wayar tsohon minista a kotu wajen sauraron shari’ar zabe

“A cikin yan kwanakin nan, yahudawan Isra’ila sun kara kai hare-hare kan al’ummar Falasdinu masu karamci inda suke ta amfani da haramtattun makamai kan bayin Allah, har ma da kai hari a asibitoci suna kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba. Abin takaici ne a ce Amurka na ba Isra'ila kudi dala biliyan 3.27 duk shekara da sunan taimakon soji."

'Yan shi'a sun soki harin cocin Gaza

A wani labarin, mun ji a baya cewa kungiyar 'Islamic Movement of Nigeria (IMN)' a ranar Juma'a ta yi zanga-zanga kan harin da aka kai cocin 'Greek Orthodox Saint Porphyrius Church' da ke Gaza yayin da rikici ke cigaba da wanzuwa tsakanin Isra'ila da Falasdinu.

Al Jazeera ta ambato ministan harkokin cikin gida na Falasdinu yana cewa harin sama da Isra'ila ta kai ya raunta 'mutane da dama' tare da jikkata wadanda suka fake a harabar cocin a Gaza.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng