Majalisar Dattawa Ta Tabbatar da Sabon Naɗin da Shugaba Bola Tinubu Ya Yi
- Majalisar dattawan Najeriya ta tantance tare da tabbatar da naɗin sabon shugaban hukumar NCC, Aminu Maida
- Hakan ya biyo bayan nazari tare da amincewa da rahoton kwamitin sadarwa na majalisar a zaman ranar Alhamis
- Kafin naɗin da shugaban ƙasa ya masa, Dakta Aminu Maida ya riƙe daraktan fasaha da ayyuka na hukumar NIBSS
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Majalisar dattawa ta tabbatar da naɗin Dokta Aminu Maida a matsayin sabon mataimakin shugaban hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC).
Majalisar ta tabbatar da naɗin bayan nazari da aminta da rahoton kwamitin sadarwa na majalisar dattawa, wanda ya tantance sabon naɗin da aka yi a NCC.
Shugaban kwamitin, Sanata Aliyu Ikra Bilbis mai wakiltar Zamfara ta tsakiya ne ya gabatar da rahoton a zaman majalisar na ranar Alhamis, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake jawabi, Sanata Bilbis ya ce naɗin Dokta Maida ya yi dai-dai da tanadin sashi na 8 (1) da ke ƙunshe a kundin dokokin hukumar sadarwa ta Najeriya 2003.
Ya ce a yayin tantance shi, kwamitin ya gano cewa Maida ya tsallake bincike kan tsaro, kuma ya mallaki abubuwan da ake bukata, gogewa, kwarewa da cancantar riƙe ofishin.
Sanata ya yi bayanin cewa ba su samu wani ƙorafi da ke adawa da naɗin da aka masa ba, bisa haka su ke ba majalisar shawarin ta amince da shi.
Bayan sauraron rahoton, nan take Majalisar dattawa ta tabbatar da naɗin Aminu Maida a matsayin mataimakin shugaban NCC.
Taƙaitaccen abinda ya kamata ku sani game da Maida
Gabanin naɗin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya masa, Dakta Aminu Maida ya riƙe matsayin daraktan sashin fasaha da ayyuka na hukumar NIBSS.
Yayi karatun digiri a ɓangaren ilimin injiniya a Imperial College London ta ƙasar Ingila kana yana da shaidar digirin digirgir daga University of Bath duk a ƙasar Burtaniya.
A yayin tantance shi, Maida ya shaida wa ‘yan majalisar cewa idan har aka tabbatar da naɗinsa, zai mayar da hankali ne wajen inganta hanyoyin sadarwa a sassan kasar nan.
Majalisar Dattawa Ta Tsoma Baki a Rigimar NLC da FG
A wani rahoton na daban kuma Majalisar dattawan Najeriya ta tsoma baki kan batun yajin aikin da ƙungiyoyin kwadago suka shiga a faɗin ƙasar nan.
Yayin zaman ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba, 2023, majalisar ta amince da kudirin da shugaban masu rinjaye ya gabatar kan yajin aikin.
Asali: Legit.ng