Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Babban Malamin Arewa, Sun Kashe Shi Bayan Karban Kuɗin Fansa

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Babban Malamin Arewa, Sun Kashe Shi Bayan Karban Kuɗin Fansa

  • Yan bindiga sun halaka wani babban Malamin Cocin ECWA wanda suka sace a Obajana ta jihar Kogi ranar Litinin
  • A wata sanarwa da Cocin ta fitar, ta bayyana cewa masu garkuwan sun kashe Fasto Musa bayan sun karɓi kuɗin fansa N1m
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, inda tace jami'ai sun baza komarsu don kamo masu hannu a kisan

Ahmad Yusuf, kwararren Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Wasu miyagun ƴan bindiga sun yi garkuwa da babban Malamin Cocin ECWA a Obajana, jihar Kogi, Fasto David Musa.

Yan bindiga sun kashe malamin da suka ɗauke a Kogi.
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Babban Malamin Arewa, Sun Kashe Bayan Karban Kuɗin Fansa Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa ƴan ta'addan sun sace Fasto Musa yayin da ya je kewaya gonarsa a garin Obajana da ke ƙaramar hukumar Lokoja ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Miyagun ƴan bindiga sun halaka babban malamin addinin da suka sace bayan karɓar kuɗin fansa a Kogi

A wata sanarwa da Cocin ta fitar, masu garkuwan sun tutunbi ƴan uwansa jim kaɗan bayan sace shi ranar Litinin, inda suka nemi a haɗa musu N20m a matsayin kuɗin fansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai bayan karban kuɗin fansan, yan bindigan ba su saki malamin ba, maimakon haka sai suka halaka shi har lahira.

Sanarwan ta ce:

"Cikin jimami da takaici tare da miƙa dukkan lamurra ga Allah, mu ke sanar da cewa waɗanda suka yi garkuwa da ɗan uwanmu, Fasto Musa David, sun kashe shi bayan karɓan fansa N1m jiya da daddare."
"Mu dage da yi wa iyalansa, coci da DCC addu'ar juriya a daidai wannan lokaci mai matuƙar wahala."

Wata majiya daga cikin danginsa ta ce tun ranar Talata aka ƙashe Faston amma sai washe gari ranar Laraba aka gano gawarsa bayan yan bindigan sun karɓi miliyan ɗaya.

Kara karanta wannan

Yan bindigar da suka sace ma'aikacin CBN da wasu 2 suna neman N10m kudin fansa

Shin jami'an tsaro sun san abin da ya faru?

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sanda reshen jihar Kogi ya tabbatar da cewa hukumarsu ta samu labarin abin da ya auku, Leadership ta ruwaito.

Ya ƙara da cewa kwamishinan ƴan sandan jihar, Onuoha Benthrand, ya umarci dakaru na musamman su bazama kamo waɗanda suka aikta kisan domin a doka ta yi aiki a kansu.

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Shugabar Karama

A wani rahoton na daban Yan bindiga sun yi garkuwa da shugabar ƙaramar hukumar Okpokwu da aka dakatar a jihar Benuwai, Amina Audu.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun sace matar ne yayin da take hanyar Naka zuwa Makurdi da safiyar ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262