Daya Bayan Daya: Jerin Johohin Najeriya da Suke da Masifar Tsadar Kayan Abinci
- Legit Hausa ta yi nazari kan jihohin da aka fi samun saukin kayan abinci, da kuma wadanda suka fi tsadar kayan abincin a fadin Najeriya
- Jihar da aka fi tsadar kayan abinci ita ce jihar Kogi, da kaso 42 cikin 100, sai kuma jihar da kayan abinci ke da sauki ita ce jihar Kebbi, da kaso 25 cikin 100
- Yan Najeriya na iya amfani da wannan kididdigar don zama haske gare su idan suka tashi sayen kayan abinci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kasar Najeriya - Hawa da saukar farashin kayan abinci ba bakon al'amari ba ne a Najeriya, sai dai, a yanzu ana cikin wani yanayi da farashin kayayyakin abinci ya tashi tun bayan janye tallafin man fetur a kasar.
Wannan ya tilasta mutane, musamman 'yan kasuwa neman mafita kan yadda za su ci gaba da samar da kayan abincin a farashin da mutane za su iya siya.
Ko a tsakanin masu siyen kayan abincin don amfani a gida, wasu kan ziyarci kasuwanni na garuruwa daban-daban, ma damar za su samu saukin farashin a can.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta yi nazari kan jihohin Najeriya da suka fi tsadar kayan abinci, har zuwa wadanda ake sayar da kayan abincin da arha.
An samar da jaddawalin ne bisa kason da kowacce jiha take da shi na hauhawar farashin kayan abincin, kamar yadda shafin kididdiga na TheCableIndex ta wallafa a shafin ta na X.
Ga jerin jihohin:
- Kogi: 42%
- Kwara: 38%
- Akwa Ibom: 37%
- Delta: 37%
- Ekiti: 37%
- Lagos: 37%
- Rivers: 37%
- Oyo: 35%
- Abia: 34%
- Ebonyi: 34%
Sauran jihohin da ke bin wadannan a tsadar kayan abinci sun hada da:
- Enugu: 34%
- Imo: 34%
- Ondo: 34%
- Osun: 34%
- Bayelsa: 33%
- Cross River: 32%
- Edo: 32%
- Anambra: 31%
- Benue: 31%
- Ogun: 31%
- Kaduna: 30%
- Plateau: 30%
- Taraba: 30%
- Abuja: 29%
- Gombe: 29%
- Niger: 29%
Jerin karshe na jihohin da ke da tsadar kayan abinci su ne:
- Zamfara: 29%
- Bauchi: 28%
- Nassarawa: 28%
- Yobe: 28%
- Adamawa: 27%
- Kano: 27%
- Katsina: 27%
- Sokoto: 26%
- Jigawa: 25%
- Kebbi: 25%
Da wannan jerin sunayen, mai karatu zai iya fahimtar inda ya dace ya sayi kayan abinci a irin wannan lokaci da kasar ke fama da tabarbarewar tattalin arziki.
Sai dai kamar yadda rahotanni suka bayyana, shugaban kasa Bola Tinubu, na hobbasa wajen ganin an farfado da tattalin arziki, ciki har da ziyartar kasar Saudiya, don nemo hannun jari.
Haka zalika, gwamnatin tarayyar ta bullo da shirye shirye da dama da take ganin za su taimaka wajen tsamo sama da 'yan Najeriya miliyan 50 daga kangin talauci.
Asali: Legit.ng