Kungiyoyin Kwadago Na NLC da TUC Sun Janye Yakin Aiki, Sun Bada Dalili
- Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun janye yajin aikin da suka shiga a daren ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba
- Sun bukaci mambobin kungiyoyin da su koma bakin aiki a ranar Alhamis, 16 ga watan Nuwamba
- An janye yajin aikin ne bayan ofishin mai ba kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya shiga tsakani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Kungiyoyin kwadago na kasa sun janye yajin aikin sai baba ta gani da suka shiga a fadin kasar wanda ya fara a ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba, domin zanga-zanga a kan dukan da aka yi wa shugaban NLC, Joe Ajaero.
Dalilin janye yajin aikin yan kwadago
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, an janye yajin aikin ne a daren ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba, bayan tattaunawa da shugabannin kungiyoyin suka yi da mai ba kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.
Ribadu ya bayyana cewa an kama mutum biyu da ke da hannu a harin da aka kai wa Ajaero.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai kuma, jaridar Vanguard ta rahoto cewa za a ci gaba da tattaunawa kan bukatun yan kwadagon.
Babban sakataren hadaddiyar kungiyar AUPCTRE, Kwamrad Sikiru Waheed, ya tabbatar da ci gaban ga manema labarai.
Ya ce:
"Biyo bayan taron hadin gwiwa na shugabannin NLC da TUC da aka kammala don yin la’akari da rokon da gwamnatin tarayya ta yi a taron da aka yi a yau a ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, taron ya yanke shawarar cewa an dakatar da yajin aikin da ke gudana.
"Kungiyoyin kwadagon suna godiya ga dukkaninku kan jajircewarku wajen ganin nasarar yajin aikin. Saboda haka ana umurtanku da ku koma bakin ayyukanku daga gobe Alhamis, 16 ga watan Nuwamba, 2023. Nagode."
Makasudin shiga yajin aikin
Ajaero da wasu shugabannin kungiyar kwadago sun yi wa garin Owerri, babban birnin jihar Imo tsinke a ranar 1 ga watan Nuwamba, don jagorantar zanga-zanga a kan gwamnatin jihar saboda zargin take hakkin ma'aikata a jihar.
Sai dai kuma, yan sanda sun kama shugaban yan kwadagon tun kafin a fara zanga-angar da kyau, sannan wasu yan dabar siyasa suka yi masa mugun duka.
Wannan lamari ya fusata yan kwadagon, wadanda daga cikin bukatunsu harda neman a tsige kwamandan da ya jagoranci harin daga aikin yan sanda sannan a hukunta shi.
Sakamakon haka ne NLC da TUC suka kaddamar da yajin aikin gama gari, lamarin da ya gurgunta harkokin kasuwanci a fadin kasar.
Majalisa ta sa baki a rigimar NLC
A baya mun ji cewa majalisar dattawan Najeriya ta shiga tsakani da nufin kawo ƙarshen yajin aikin da ma'aikatan Najeriya suka fara tun ranar 14 ga watan Nuwamba, Channels tv ta rahoto.
A ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba, Majalisar dattawan ta yi kira ga manyan ƙungiyoyin ƴan kwadago, NLC, TUC da malaman jami'a (ASUU) su hakura su janye yajin aiki.
Asali: Legit.ng