CBT: Muhimman Abubuwa 4 da Ya Kamata Ku Sani Kan Sabon Tsarin Rubuta Jarrabawar WAEC

CBT: Muhimman Abubuwa 4 da Ya Kamata Ku Sani Kan Sabon Tsarin Rubuta Jarrabawar WAEC

  • Hukumar WAEC ta sanar da sauya salo daga zana jarabawar a takarda zuwa amfani da kwamfuta (CBT) ga daliban SSCE a Najeriya
  • Amfani da komfuta wajen zana jarabawar, zai fara ne a watan Fabrairu 2024, ga dalibai masu zaman kansu, a cewar majalisar jarrabawar
  • CBT za ta kunshi tambayoyi na canki-caka, tare da nau'ikan tambayoyin da ke bukatar amsar zube, da kuma tambayoyin 'aiki da kanka'

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Lagos, Najeriya- Hukumar shirya jarabawar Afirka ta Yamma (WAEC), ta ce za ta fara amfani da tsarin na'ura mai kwakwalwa (CBT) wajen gudanar da jarrabawar kammala sakandare (SSCE).

Hukumar jarrabawar ta bayyana hakan ne a ranar Litinin, 13 ga watan Nuwamba, cewar za a yi watsi da tsarin zana jarabawar ta hanyar amfani da takarda da fensir.

Kara karanta wannan

CBT: WAEC ta fito da sabon tsarin rubuta jarrabawa na zamani

WAEC CBT
Hukumar Jarrabawar Afirka ta Yamma (WAEC) za ta fara amfani da tsarin Jarabawar Kwamfuta (CBT) don gudanar da jarrabawar shaidar kammala sakandare (SSCE). Hoto: Olukayode Jaiyeola/NurPhoto
Asali: Getty Images

Wannan rubutu, zai yi bayani kan duk abin da ya kamata ku sani game da WASSCE CBT, don dalibai masu zaman kansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Yaushe WAEC za ta fara amfani da tsarin CBT?

Za a fara amfani da tsarin CBT ga dalibai masu zaman kansu da za su zana jarrabawar kammala sakandare ta yammacin Afirka a watan Fabrairun 2024.

Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mukaddashin shugaban hulda da jama’a na WAEC, Moyosola F. Adesina.

2. Ta yaya za a gudanar da WASSCE CBT?

A cewar WAEC, dalibai za su amsa sashen canki-canka a komfuta, sai kuma sashen rubutun zube da 'aiki da kanka' zai gudana a kwamfuta da kuma takarda.

Tsarin CBT na WAEC kawai yana nufin cewa ba za a sake yin amfani da tambayoyi a jikin takardu a dakunan zana jarabawa ba.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Kogi: Murtala Ajaka ya yi watsi da sakamakon INEC, ya bayyana mataki na gaba

Za a sanya tambayoyin jarrabawar ne a kan kwamfuta yayin da za a ba daliban littafan rubuta amsar tambayoyin.

3. A ina za a gudanar da jarrabawar WASSCE CBT?

A cewar WAEC, za a gudanar da jarrabawar tsarin CBT ne a biranen kasar nan.

Hukumar jarrabawar ta kara da cewa ta ba da dama ga masu bukata ta musamman a wannan tsarin na zana jarabawar.

4. WASSCE CBT: Yaushe za a fara rajista?

WAEC ta ce za a fara rajistar jarrabawar ne a ranar Litinin 18 ga watan Disamba, 2023.

Domin fahimtar da dalibai kan sabon tsarin, hukumar ta ce za a gudanar da jarrabawar gwaji a watan Fabrairun 2024, kafin fara babbar jarrabawar.

Ya shawarci masu neman zana jarabawar da su inganta fasahar su ta amfani da kwamfuta kuma su kasance cikin shiri sosai don yin amfani da sabuwar fasahar.

CBT: WAEC ta fito da sabon tsarin rubuta jarrabawa na zamani

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan wasu ‘yan bindiga sun bindige shugaban jam’iyyar siyasa a jihar Anambra

Hukumar shirya jarabawar kammala sakandire ta Afrika ta Yamma (WAEC), ta sanar da amincewa da tsarin jarabawar da za a rinka yi ta hanyar amfani da kwamfuta (CBT), don gudanar da jarrabawar kammala sakandare (SSCE).

WAEC: "Tsarin CBT ne mafi sauki", in ji Ogunbayi, masani kan ilimi

A wani labarin, shugaban hukumar kula da ayyukan ilimi ta MIMS, Prince Adesegun Ogungbayi, ya yi maraba da shirin da WAEC ta yi na bullo da tsarin CBT wajen gudanar da jarrabawar ta.

Sai dai kuma, Prince Ogungbayi wanda ya yi magana da jaridar Legit.ng ya bayyana wasu abubuwa da yake hange game da tsarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.