An Tafka Babban Rashi Bayan Mutuwar Matashin Mawaki Mai Shekaru 28 a Najeriya

An Tafka Babban Rashi Bayan Mutuwar Matashin Mawaki Mai Shekaru 28 a Najeriya

  • Ana cikin jimami bayan rasuwar wani matashi shahararren mawaki mai suna Oladipopu Olabode Oladimeji a jiya Talata
  • Marigayin mai shekaru 28 wanda aka fi sani da Oladips ya rasu a daren jiya Talata 14 ga watan Nuwamba
  • Wannan na zuwa ne watanni kadan baya mutuwar mawaki 'Mohbad' wanda mutuwarshi ta jawo cece-kuce a Najeriya

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - An yi babban rashi bayan rasuwar shahararren matashin mawaki mai suna Oladipopu Olabode Oladimeji.

Marigayin wanda aka fi sani da Oladips ya rasu ya na da shekaru 28 kacal a duniya, Legit ta tattaro.

Matashin mawaki 'Oladips' ya rasu ya na da shekaru 28
Matashin ya rasu a daren jiya ya na da shekaru 28. Hoto: @oladipsoflife.
Asali: Instagram

Yaushe matashin ya rasu?

The Nation ta tattaro cewa mawakin ya rasa ransa a daren jiya Talata 14 ga watan Nuwamba bayan an garzaya da shi asibiti.

Kara karanta wannan

Innalillahi, Wani babban Sarki mai martaba a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kamfaninsu ya fitar a shafin Instagram.

Sanarwar ta ce:

"Muna bakin cikin sanar da ku cewa Oladipopu Olabode da aka fi sani da Oladips ya rasu jiya Talata 14 ga watan Nuwamba da yammaci.
"Oladips ya rasu da misalin karfe 10:14 na dare, har yanzu muna cikin jimamin mutuwarshi.
"Fiye da shekaru biyu ya na fama da matsalar bai fada wa kowa ba, za a sanar da shirye-shiryen binne shi nan ba da jimawa ba."

Yaushe Mohbad ya rasu?

Mutuwar matashin na zuwa ne watanni biyu bayan rasuwar matashi 'Mohbad' wanda ya mutu ya na da shekaru 27.

Mutuwar 'Mohbad' ta jawo kace-nace inda ake zargin kashe shi aka yi da gan-gan ba mutuwar Allah da Annabi ba.

Daga bisani da korafe-korafe suka yi yawa sai da aka tono shi a kabari don gudanar da bincike.

Kara karanta wannan

Mahara sun bukaci miliyan 53 kudin fansar malamin addini da wasu mutum 2 a jihar Arewa

Dan wasan kwaikwayo, Samanja ya rasu

A wani labarin, Shahararren dan wasan kwaikwayo a Arewacin Najeriya, Alhaji Usman Baba Pategi ya riga mu gidan gaskiya a jihar Kaduna.

Marigayin wanda aka fi sani da Samanja mazan fama ya rasu ne bayan fama da doguwar jinya a Kaduna.

Samanja wanda ya kasance tsohon soja ne ya shafe shekaru da dama ya na wasan kwaikwayo a gidan rediyon Najeriya ta Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.