Gwamnan PDP Ya Jawo Wa Kansa, Ya Shiga Babbar Matsala Kan Korar Wasu Jiga-Jigan Gwamnati

Gwamnan PDP Ya Jawo Wa Kansa, Ya Shiga Babbar Matsala Kan Korar Wasu Jiga-Jigan Gwamnati

  • Gwamna Adeleke ya jawo wa kansa matsala bayan ya kori shugabanni da mambobin majalisar gudanarwa na hukumomi 4 a Osun
  • Waɗanda gwamnan ya kora sun kai ƙara gaban Kotun ɗa'ar ma'aikata, inda suka ce an kore su gabanin wa'adin su ya ƙare
  • Sun nemi a tilastawa Gwamnan ya maida su bakin aiki ko kuma ya biya su ragowar albashin da ya rage

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Osun - Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya gamu da babban cikas yayin da aka kai ƙararsa gaban Kotun ɗa'ar ma'aikata kan korar wasu jiga-jigai daga aiki.

Gwamna Adeleke na jihar Osun.
Gwamna Adeleke Na Jihar Osun Ya Shiga Matsala Kan Korar Wasu Jiga-Jigan Gwamnati Hoto: Ademola Adeleke
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an maka Gwamna Adeleke na PDP a gaban Kotu ne kan rushe majalisar gudanarwa na wasu hukumomi ba bisa ƙa'ida ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya gano gaskiya, ya umarci wasu ma'aikatan Gwamnati su yi murabus

Gwamnan ya tsige shugabanni da mambobin majalisar gudanarwar hukumomin Gwamnatin Osun huɗu, waɗanda magabacinsa ya naɗa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumomin da Gwamna Adeleke ya rushe majalisarsu sun haɗa da, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Osun (OSSIEC), hukumar kula da harkokin shari'a, hukumar jin daɗin ma'aikata da hukumar kula da ayyukan majalisar dokoki.

Bayan haka, Adeleke ya naɗa sabbin waɗanda zasu jagoranci hukumomin guda huɗu bayan majalisar dokokin jihar Osun ta amince da naɗinsu ranar Litinin.

Su waye suka maka Gwamna Adeleke a Kotu?

Shugabannin waɗannan hukumomi da mambobin gudanarwa da Gwamnan ya kora ne suka shigar da ƙara daban-daban gaban Kotun ɗa'ar ma'aikata mai zama a Ibadan.

Sun roƙi Kotun ta ayyana matakin korarsu daga aiki a matsayin haramun, ɗabi'a mara kyau da kuma saɓa wa kundin tsarin mulki.

Ta bakin lauyansu, Kunle Adegoke, SAN, ya roki kotun da ta tilasta wa gwamnati da jami’anta su dawo da shuwagabannin hukumomin domin cika wa'adin shekaru biyar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare motar Gwamnatin jihar arewa, sun tafka mummunar ɓarna tare da sace mutane

Sai dai uku daga cikinsu da wasu mambobin sun bukaci kotun ta umarci wadanda ake kara da su biya su albashi da alawus din su daga watan Nuwamba 2023 har zuwa karewar wa’adinsu.

Wadanda ake tuhuma a ƙarar sun hada da gwamnan Osun, Antoni Janar kuma kwamishinan shari’a na jihar; Kwamishinan kudi da majalisar dokokin jihar Osun, rahoton Daily Post.

Gwamnan Sokoto ya umarci wasu ma'aikata su yi murabus

A wani rahoton na daban Gwamna Ahmed Aliyu ya umarci sakatarorin kananan hukumomin jihar Sakkwato su aje aikin Gwamnati.

Ya ce tunda ta tabbata muƙaman da aka naɗa su na siyasa ne, ya zama wajibi su bi doka duk wanda ke aikin Gwamnati ya aje shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262