Gwamnan PDP a Arewa Ya Sanya Dokar Ta Baci a Bangaren Ilimi, Ya Dauki Mataki Daya Tak Kan Makarantu
- Gwamna Dauda Lawal ya sanya dokar ta baci a bangaren ilimi a jihar Zamfara baki daya don ceto jihar daga durkushewa
- Gwamnan har ila yau, ya kwace lasisin dukkan makarantu masu zaman kansu da ke jihar don inganta harkar ilimi
- Dare ya bayyana haka ne a yau Talata 14 ga watan Nuwamba yayin jawabi ga 'yan jihar inda ya koka kan lalacewar bangaren ilimi
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Zamfara - Gwamna Dauda Lawal Dare na jihar Zamfara ya sanya dokar ta baci a bangaren ilimi a jihar baki daya.
Gwamnan ya kuma kwace lasisin makarantu masu zaman kansu a jihar don ceto harkar ilimi.
Wane mataki Dauda Lawal ya dauka a bangaren ilimi?
Dare ya bayyana haka ne a yau Talata 14 ga watan Nuwamba yayin jawabi ga 'yan jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya nuna damuwarshi yadda harkar ilimi ta tabarbare tun daga matakin firamare har zuwa na Jami'a, cewar Channels TV.
Ya ce:
"Don tabbatar da inganta harkar ilimi a jihar Zamfara, gwamnati ta kwace lasisin dukkan makarantu masu zaman kansu a jihar.
"Hakan zai taimaka wurin tabbatar da cewa dukkan makarantu masu zaman kansu sun inganta yadda suke gudanar da ayyukansu."
Wane martani kakakin gwamnan ya yi kan dokar?
Dadi da kari, kakakin gwamnan, Sulaiman Idris ya ce matakin gwamnan na kafa dokar ta baci a harkar ilimi na daga cikin alkawuran da ya dauka wa jama'ar jihar.
Sanarwar ta ce:
"A jawabin Gwamna Dauda Lawal a yau Talata, ya sanya dokar ta baci a bangaren ilimi a jihar Zamfara."
Hakan a daga cikin alkawuran da gwamnan ya yi yayin da ke kamfe a yakin neman zabe a jihar, cewar Tribune.
Matawalle ya samu yabo daga 'yan Najeriya
A wani labarin, matasan Najeriya sun kwarara yabo ga karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle kan samar da tsaro.
Matasan wadanda ke wakiltar kungiyar rajin kare dimukradiyya sun yaba wa Matawalle kan inganta tsaro da ya yi a fadin kasar baki daya.
Kungiyar ta yabawa Shugaba Tinubu wurin nada Matawalle mukamin minista inda suka bukaci 'yan Najeriya su yi watsi da karairayi na rashin tsaro a ƙasar.
Asali: Legit.ng