Tinubu Ya Bayyana Tarin Gwaramar da Shugabannin da Suka Gabacesa Suka Bar Wa Gwamnatinsa

Tinubu Ya Bayyana Tarin Gwaramar da Shugabannin da Suka Gabacesa Suka Bar Wa Gwamnatinsa

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya koka kan tarin basussukan da shugabannin da suka gabace sa suka bari
  • Shugaban ƙasar ya yi nuni da cewa ƙasar nan na fama da giɓi sosai a fannin tasoshin jiragen ruwa, wutar lantarki da ayyukan noma
  • Shugaba Tinubu wanda ya ce ba wani uzuri da zai nema ya bayyana cewa akwai kadarorin da ya gada daga magabatansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Saudiyya - Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin sa ta gaji manyan basussuka amma kuma ta gaji kadarori daga daga waɗanda suka gabace shi.

Tinubu wanda ya yi magana a daren ranar Litinin a birnin Makkah na Saudiyya, ya koka kan yadda Najeriya ke fama da matsanancin giɓi a bangaren tashoshin jirgin uwa da samar da wutar lantarki, da kuma ayyukan noma.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu da mukarrabansa sun daura haramar yin Umrah a ziyararsu ta Saudiyya

Shugaba Tinubu ya yi magana kan basussukan da ya gada
Shugaba Tinubu ya koka kan basussukan da ya gada Hoto: @DOlusegen
Asali: Twitter

Sai dai shugaban na Najeriya ya ce ba wani uzuri da zai nema, kamar yadda wata sanarwa da kakakinsa Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Talata ta bayyana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mun gaji manyan basussuka amma har da kadarori daga magabatan mu. Ba mu da wani uzuri." A cewar Tinubu.
“Akwai sassa da yawa cike da damar saka hannun jari ga masu saka hannun jari masu wayo. Samun kuɗi da tabbaci na iya zama cikas a wasu lokuta. Kuna iya shigowa wajen. Muna ganin ku a matsayin masu ba da taimako."
"Kun yi tarayya da mu a baya. Muna so mu haɓaka shi a yanzu kuma mu yi abubuwa da yawa tare da babban buri da hangen nesa mai haske."

Tinubu ya halarci taro a Makkah

A taron na Makkah, Shugaba Tinubu ya kuma cigaba da tattaunawa game da ayyukan samar da ababen more rayuwa na biliyoyin daloli daga bankin raya ƙasa na Musulunci don samar da kuɗaɗen gudanar da ayyukan more rayuwa da dama a matakin tarayya da na ƙananan hukumomi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Kano: Kotun musulunci ta umurci magidanci ya karbi ɗan da ya ke kokwanton ba nasa bane

Wannan cigaban ya samo asali ne daga wata muhimmiyar tattaunawa kan saka hannun jari da aka yi tsakanin Shugaba Tinubu da mataimakin shugaban bankin raya ƙasa na Musulunci, Dokta Mansur Muhtar.

Buhari Ya Tsiyata Ƙasa

A wani labarin kuma, mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya ƙarbi ƙasar nan a cikin wani mawuyacin hali.

Ribadu ya bayyana cewa sai da tsohon shuagaban ƙasa Muhammadu Buhari ya gama tsiyata ƙasar nan sannan ya miƙa ta a hannun Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng