Tsaro Ya Inganta, Yan Najeriya Sun Kwarara Yabo Ga Matawalle Kan Kawo Sauyi, Sun Ba da Misali

Tsaro Ya Inganta, Yan Najeriya Sun Kwarara Yabo Ga Matawalle Kan Kawo Sauyi, Sun Ba da Misali

  • Yayin da ake ci gaba da korafi kan tsaro a kasar, Ministan Tsaro, Bello Matawalle ya samu yabo daga ‘yan Najeriya
  • Matasa da ke Kungiyar masu kishin kasa sun yabawa Ministan inda suka ce an samu ingantaccen tsaro a kasar
  • Kungiyar ta bayyana haka ne a karshen wannan mako a birnin Abuja inda ta yabawa Tinubu kan inganta tsaro

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – ‘Yan Najeriya da dama sun yabi karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle kan inganta tsaro a kasar baki daya.

Matasa daga ko wane bangare a kasar sun yaba wa karamin Minitan yayin da aka samu ingantaccen tsaro a kasar, Tribune ta tattaro.

Matasan Najeriya sun yabi Matawalle kan inganta tsaro a kasar
Matasa sun yi martani kan Minista Matawalle. Hoto: Badaru A, Bello Matawalle.
Asali: Twitter

Mene matasan ke cewa kan Matawalle?

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu da mukarrabansa sun daura haramar yin Umrah a ziyararsu ta Saudiyya

Matasan karkashin Kungiyar Masu Rajin Kishin Kasa sun kuma yabi babban Minista Badaru Abubakar a kokarin da suke yi na tabbatar da tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar wacce ta kunshi matasan daga dukkan bangarorin kasar ta bayyana haka a karshen mako a birnin Tarayya Abuja.

Wakilin kungiyar daga Arewa maso Yamma, Kwamred Muh’d Zaharaddeen ya ce a yanzu hanyoyinsu sun samu tsaro sabanin lokacin da ba a nada su ministoci ba.

Har ila yau, wakilin kungiyar daga Kudu maso Yammacin kasar, Abiola Peter ya ce tun bayan nada su mukamai komai ya koma daidai.

Wane kira suka yi wa Tinubu?

Ya ce a jihar Oyo akwai wani gari da ake kira Ighobo kafin zuwansu garin babu zaman lafiya amma yanzu ya zama tarihi, cewar Leadership.

Takawaransu daga Arewa ta Tsakiya, Muhammad Hamza ya ce kafin nadin nasu, yankinsu na fama da matsalolin sace mutane da fashi amma yanzu ya wuce.

Kara karanta wannan

Ajaero: Ka da ku kuskura ku matso kusa da ma'aikata ta, Ministan Tinubu ya tura gargadi ga NLC

Sannan wakilinsu daga yankin Neja Delta, Abraham Ekokotu ya ce ya na kira ga shugaban kasa da sauran mutane da su yi watsi da korafe-korafen da ake yi kan Matawalle.

Yayin da wakili daga Arewa maso Gabashin kasar, Awal Aliyu ya ce a yanzu idan aka duba jihohin Borno da Yobe da Bauchi kowa ya san an samu sauyi.

Matawalle ya yi wa masu zabe alkawari

A wani labarin, Karamin Ministan Tsaro Bello Matawalle ya ba da tabbacin samun ingantaccen tsaro a lokacin zabe.

Matawalle ya ce kowa ya fita ya kada kuri’arsa ba tare da wani tsoro ba a jihohin da za a yi zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.