Yanzu nan: ASUU Tayi Umarnin Shiga Yajin Aiki, Malaman Jami’a Sun Yi wa 'Yan NLC Biyayya
- Kungiyar ASUU ta amsa kiran da shugabannin NLC da TUC su ka yi na shiga yajin-aiki daga tsakar daren Talatar nan
- Shugaban kungiyar malaman jami’a, Emmanuel Osodeke ya aika takarda zuwa ga ‘Yan ASUU cewa su dakatar da zuwa aiki
- Farfesa Osodeke ya ce ASUU ta na cikin ‘ya ‘yan kungiyar NLC, saboda haka tana goyon bayan matakin nan da ta dauka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Kungiyar ASUU ta malaman jami’a ta umarci ‘ya ‘yanta su ka shiga yajin-aikin da kungiyoyin NLC da TUC su ka kira a yau.
Shugaban ASUU na kasa, Emmanuel Osodeke ya aika da wasika zuwa ga duka rassan kungiyar, Premium Times ta kawo rahoton.
Sabon yajin-aiki a jami'o'in gwamnati
Farfesa Emmanuel Osodeke ya rubuta takarda zuwa ga shugabannin ASUU na yankuna da jihohi cewa su shiga yajin-aikin da aka tafi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kungiyar malaman jami’an kasar yake cewa ya kamata su bi sahun kungiyar ‘yan kwadago domin suna cikin ‘ya ‘yanta.
Rahoto ya ce wasikar Osodeke ta nuna shiga yajin-aikin da aka fara zai taimaka wajen kare ma’aikata da shugabannin kungiyoyinsu.
Yajin-aiki saboda an jibgi Joe Ajaero
A dalilin lakadawa Joe Ajaero duka da aka yi, NLC da TUC ta nemi ‘ya ‘yanta su daina aiki.
Shugabannin kungiyoyin kwadagon da ‘yan kasuwa sun aika takarda zuwa ga sauran ma’aikata cewa su dakatar da ayyuka daga yau.
Wasikar shugaban ASUU kan yajin-aiki
"A matsayin ‘ya ‘yan kungiyar NLC, ana umartar duka ‘ya ‘yanmu su bi NLC wajen kare hakkin ma’aikatan Najeriya da shugabannin kungiyar.
Shugabannin yankuna da na rassa su gaggauta tattara ‘yan kungiyarmu domin shiga wannan yajin-aiki."
- Farfesa Emmanuel Osodeke
Dama can kungiyar ba ta goyon bayan wasu tsare-tsare gwamnatin Bola Tinubu musamman na cire masu kudi a baya-bayan nan.
Shugabannin jami’a sun ce ba su yi na’am da a rika zaftare 40% na kudin shigansu ba.
Wasu ma’aikata ba su shiga yajin-aiki ba
Legit ta zanta da wasu ma’aikata a Abuja da Kaduna, wadanda su ka ce sun fita wuraren aiki, ba su yi biyayya ga NLC da TUC ba.
Wani ma’aikaci da ke jami’ar ABU Zariya, Malam Salihu Umar ya fadawa Legit cewa yajin-aikin da aka sanar bai hana su zuwa ofis ba.
“Mu muna zuwa ofis, ga mu nan haka a wurin aiki. Kowa ya je aiki saboda mun ji kotu ta ce bai halatta a tafi ba.
Ba mi sani ba watakila zuwa gobe (ranar Laraba), yajin-aikin ya yi tasiri.”
- Ma'aikaci
Tinubu ya soki kungoyoyin NLC da TUC
Rahoto ya zo cewa Fadar shugaban kasa ta ce ta ji takaicin jin matakin NLC da TUC na kiran ‘ya ‘yansu su shiga yajin-aiki daga tsakar dare.
Bayo Onanguga ya ce Shugabannin NLC na neman taso gwamnati a gaba ne duk da hukuncin kotu ya haramta wannan yajin-aikin na su.
Asali: Legit.ng