NLC Ta Rubutawa Ma’aikatan Wuta da Makarantu Takardar Dunguma Yajin Aiki a Najeriya

NLC Ta Rubutawa Ma’aikatan Wuta da Makarantu Takardar Dunguma Yajin Aiki a Najeriya

  • Kungiyar ‘yan kwadago da ‘yan kasuwa sun shiga yajin-aiki a sakamakon abin da ya faru da Joe Ajaero kwanakin baya
  • A gabanin zaben Gwamna a jihar Imo, aka samu wasu miyagu su ka yi wa shugaban NLC na kasa mugun duka
  • Abin da ya faru da Kwamred Ajaero ya fusata ma’aikata, musamman bayan gwamnati tayi watsi da jerin bukatunsu

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Kungiyar ‘yan kwadagon Najeriya ta umarci ma’aikatanta da su fara yajin-aikin sai baba-ta-gani a duk fadin kasar nan.

Rahoton da aka samu daga Daily Trust ya ce yajin-aikin ya fara ne daga daren yau, tun daga 12:00 na tsakar daren Talatar nan.

Cin zarafin shugaban NLC na kasa, Kwamred Joe Ajaero kafin zaben gwamna a jihar Imo ne abin da ya jawo wannan yajin-aiki.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kungiyoyin Kwadago sun shiga yajin aiki sai baba ta gani kan lakadawa shugaban NLC duka

'Yan kwadago
NLC: 'Yan kwadago sun fara yajin-aiki Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kowane ma'aikaci zai shiga yajin-aikin?

NLC ta ‘yan kwadago da kungiyar TUC ta ‘yan kasuwa ta bukaci duka wadanda su ke karkashinta su bi sahu, a tsaida ayyuka daga yau.

Punch ta ce TUC da NLC sun rubutawa ma’aikatan wutan lantarki, makarantu da sauran wurare cewa a shiga yajin-aikin daga yau.

Wannan ita ce matsayar da shugabannin majalisar kolin kungiyoyin su ka dauka a kasar.

Meya jawo NLC da TUC su ka tafi yajin-aiki?

Da yake magana da manema labarai a gidan kwadago da ke garin Abuja, shugaban TUC, Festus Osifo ya ce sam babu wani ja da baya.

Kwamred Festus Osifo yake cewa za su yi ta yajin-aiki ne har sai gwamnatoci a kowane mataki sun fadaka, sun yi abin da ya dace.

An ci zarafin shugaban NLC a Imo

Premium Times ta ce Osifo ya yi mamakin yadda jami’an tsaro su ka gagara cafke wadanda ake zargin su na da hannu wajen jibgar Ajaero.

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da su ka taimaki APC, suka Kashe LP da PDP a zaben Gwamnan Imo

Ma’aikatan sun bukaci tsige shugaban ‘yan sandan yankin da su ke zargin ya jagoranci dukan da aka lakadawa jagoran ‘yan kwadago.

Haka zalika ‘yan kwadagon sun nemi a cafke wani Chinaza wanda su ka ce sanannen ‘dan ta’adda ne a Imo, har yau ba ayi wannan ba.

LP, PDP sun sha kashi a zaben Imo

Ku na da labari cewa jam'iyyar APC tayi wa Samuel Anyanwu, Athan Achonu da Lincoln Ogunewe bugun gangar coci a zaben na jihar Imo

Karya ‘yan adawa da rashin karfin jam’iyyar PDP ya taimakawa Gwamnan Imo watau Hope Uzodinma wajen lashe zaben tazarcen bana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng