Tinubu Ya Bada Umurnin a Janye 'Yan Sanda Masu Tsaron Manya a Najeriya
- Shugaban kasa Bola Tinubu, ya bayar da umurnin janye jami’an ‘yan sandan Najeriya daga ayyukan tsaro ga manyan mutane (VIPs)
- Shugaban ya ce an yanke shawarar yin hakan ne domin baiwa ‘yan sanda damar dawo da matsayinsu a tsarin ‘tsaro na cikin gida Najeriya
- Ma’aikatar harkokin ‘yan sanda na cikin wani mawuyacin hali, da kuma illar rashin kula da su na tsawon shekaru da ya jawo musu cikas wajen cika aikin su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Karamin ministan harkokin ‘yan sanda, Imaan Suleiman-Ibrahim, ta bayyana cewa, hukumar rundunar ‘yan sanda za ta aiwatar da umarnin shugaban kasa Bola Tinubu na janye jami’an ‘yan sanda daga ayyukan tsaro ga manyan mutane (VIPs).
Haka zalika, ministar ta ce gwamnatin Tinubu za ta samar da dabarun gudanar da aikin ‘yan sanda da dai sauransu.
Za mu dawo da darajar aikin dan sanda - Minista Imaan
Ministar ta bayyana hakan ne a ranar Litinin, a yayin wani taron koli na kwanaki biyu da aka shirya a ma’aikatar harkokin ‘yan sanda.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta yi nuni da cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya da ma’aikatar harkokin ‘yan sanda na cikin wani mawuyacin hali, da kuma illar rashin kula da su na tsawon shekaru da ya jawo musu cikas wajen cika aikin su.
Ta kara da cewa, ma'aikatar ta himmatu wajen daidaita kokarinta na bayar da gudummuwa don ganin an cimma burin shugaban kasa, na daga darajar aikin dan sanda.
Abin da Ministar ta ce game da tsare-tsaren Shugaba Tinubu
Imaan Suleiman-Ibrahim ta ce:
“Kamar yadda kuka sani, muhimman ayyukanmu sun hada da aiwatar da umarnin shugaban kasa kan janye jami’an ‘yan sanda daga ayyukan tsaro ga manyan mutane (VIPs), da samar da dabarun ayyuka ga yan sanda, da dai sauransu."
"Bai kamata mu kalli wadannan dokoki da tsare-tsaren a matsayin ayyuka kawai ba, amma a matsayin sauye-sauyen da za su iya inganta tsaron Najeriya.”
IGP Olukayode Egbetokun ya magantu kan tsare-tsaren 'yan sanda
Ko a watan Yuni, Legit Hausa ta ruwaito cewa, bayan kafa runduna ta musamman ta mutum 40,000, babban sufeton ‘yan sanda, Olukayode Egbetokun, ya bayyana shirin janye jami’an rundunar ‘yan sanda daga aikin gadin manyan mutane.
Egbetokun ya yi maganar ne a lokacin da yake ganawa da shugabannin Squadron da kwamandojin dabarar yaki a hedikwatar rundunar,
Ya ce ana shirin yin hakan ne domin baiwa ‘yan sanda damar dawo da matsayinsu a tsarin ‘tsaro na cikin gida Najeriya.
Asali: Legit.ng