Nasara Daga Allah: Yan Bindiga Sun Mutu Yayin da Dakarun Sojoji Suka Buɗe Musu Wuta a Jihar Arewa
- Sojojin Najeriya sun ragargaji ƴan bindiga a garuruwa da dama a jihar Kaduna, sun yi nasarar kashe wasu, sun kwato makamai
- Mataimakin daraktan yaɗa labarai, Musa Yahaya, ya ce sojojin sun samu wannan nasara ne yayin da suka fita aikin shara ranar Lahadi
- Kwamandan rundunar sashi na 1 ya yaba da namijin kokarin dakarun sojin kana ya roƙe su da kar su yi sanyi har su samu galaba
Ahmad Yusuf, kwararren Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Dakarun sojin sashi na 1 kuma sojojin Operation Whirl Punch sun samu nasarar sheƙe yan bindigan daji uku a samamen shara a ƙaramar hukumar Kajuru a Kaduna.
Mataimakin daraktan yaɗa labaran rundunar, Laftanar Kanal Musa Yahaya ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Yadda Sojoji suka farmaki ƴan bindiga
Ya ce gwarazan sojojin sun kai farmakin sharar ne ranar Lahadi a dajin Maro-Chibiya da ke yankin Kajuru, kuma yayin haka suka yi musayar wuta da ƴan bindigan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, sojojin sun yi nasarar halaka ɗan bindiga ɗaya nan take, yayin da sauran suka ari na kare ɗauke da raunukan harbin bindiga.
Musa ya bayyana cewa yayin wannan artabu, sojojin sun kwato bindiga ƙirar AK-47, da wacce ake ƙera wa a gida guda ɗaya, da alburusai da wayar hannu guda ɗaya.
A rahoton Channels tv, kakakin rundunar ya ce:
"Dakarun soji sun ƙara kai farmaki makamancin wannan a ƙauyukan Kawara da Filin Jalo a ƙaramar hukumar Igabi, inda nan ma suka sheƙe ɗan bindiga ɗaya, suka kwato makamai."
"Bugu da ƙari, dakarun rundunar sun kuma kai samame kauyukan Mai- Kulu- Gwanda, Rafin Gora, Funtua Badadi da Kabawa duk a yankin Birnin Gwari, suka kashe ɗan bindiga kana suka kwato Babur a Radiyo."
"Kwamandan rundunar sojin sashi na 1 da Operation Whirl Punch ya yaba da ƙwazon jami'an kana ya soƙe su kara zage dantse har sai sun kawar da ƴan ta'adda baki ɗaya a yankin."
Sojoji sun halaka yan bindiga sama da 100
A wani rahoton kuma Dakarun sojin Najeriya sun samu nasarar halaka ƴan ta'adda 113, kuma sun kamo wasu 300 a makon da ya gabata a faɗin kasar nan.
Daraktan yaɗa labarai na rundunar, Manjo Janar Edward Buba, ya ce bayan haka sojojin sun kwato mutane 91 da aka yi garkuwa da su.
Asali: Legit.ng