Yan bindiga Sun Shiga uku, Ɗan majalisar PDP Ya Bai Wa Jami'an Tsaro Kayan Aiki, Ya Tallafawa Mata
- Honorabul Umar Yusuf yabo ya raba wa mutanen mazaɓarsa da hukumomin tsaro babura 200
- Ɗan majalisar tarayyan ya kuma bai wa mata 2,000 jarin Naira N50,000 kana ya raba wa wasu matan firiza don su fara sana'a
- Da yake jawabi, ya ce wannan somin taɓi ne kuma yana ɗaya daga cikin aƙawurran da ya ɗauka lokacin kamfe
Ahmad Yusuf, kwararren Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Sokoto - Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Yabo-Shagari, Umar Yusuf Yabo, ya bayar da tallafin babura 200 ga hukumomin tsaro da wasu mutane a mazaɓarsa.
Ya kuma baiwa mata 2,000 jari tare da gina famfunan ruwa 50 da kuma injinan samar da wutar lantarki mai karfin 2.5KVA guda 50 ga manoma da masallatai a yankunan biyu.
Bai tsaya iya nan ba, Dan majalisar ya kuma raba kayan makaranta 500 da litattafan rubutu 5,000 ga daliban firamare, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake jawabi a wurin taron wanda ya gudana a garin Yabo ranar Litinin, Yusuf ya ce wannan tagomashin na cikin alkawuran da ya yi wa al’ummar mazabar a lokacin kamfe.
Ɗan majalisar ya ce:
"A lokacin yakin neman zabe, na yi wa al’ummarmu alkawarin kawo sauyi mai kyau domin Yabo/Shagari ta rasa wakilci na gari a zauren majalisar wakilai na tsawon shekaru da dama."
"Sabida haka abin da kuke gani yau ba komai bane illa mafarin kyawawan abubuwan da ke kan hanya."
Ya raba wa nata jarin N50,000
A cewarsa, kowacce daga cikin mata 2000 za ta samu tallafin Naira 50,000, inda ya kuma kara da cewa, akwai wasu mata 50 da za a ba su kyautar firiza kowace ɗaya.
'Dan Majalisar APC ya rantse da Allah, ya ce zasu tuhumi Tinubu kan yadda aka yi da kuɗin tallafin fetur
A rahoton The Sun, ya ci gaba da cewa:
"Na kuma miƙa koken matsalar wutar lantarki ga majalisa saboda yankunan Yabi da Shagari sun jima cikin duhu tsawon shekaru. Na muku alƙawarin hasken wutar lantarki zai dawo nan bada daɗewa ba."
Ijaw ta kudu ce zata raba gardama a Bayelsa
A wani rahoton na daban Ana hasashen ƙaramar hukuma ɗaya ce zata raba gardama a zaɓen Gwamnan jihar Bayelsa tsakanin APC da PDP.
Zuwa yanzun INEC ta karɓi sakamakon kananan hukumomi 7 kuma Gwamna Diri na PDP ne ke kan gaba da tazarar ƙuri'u 58,577.
Asali: Legit.ng