CBT: WAEC Ta Fito Da Sabon Tsarin Rubuta Jarrabawa Na Zamani
- Hukumar zana jarabawar WAEC, ta sanar da amincewa da tsarin jarabawar da za a rinka yi ta hanyar amfani da kwamfuta (CBT)
- A cewar sanarwar, za a fara amfani da sabuwar fasahar ne ga daliban da za su zana jarrabawar WASSCE masu zaman kansu a watan Fabrairun 2024
- Hukumar mai shekaru 72 da kafuwa, ita ce hukumar da ta fi tsufa a yankin Afirka ta Yamma
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Yaba, jihar Legas - Hukumar shirya jarabawar kammala sakandire ta Afrika ta Yamma (WAEC), ta sanar da amincewa da tsarin jarabawar da za a rinka yi ta hanyar amfani da kwamfuta (CBT), don gudanar da jarrabawar kammala sakandare (SSCE).
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mukaddashin shugaban sashin hulda da jama’a na WAEC, Moyosola Adesina, kuma aka raba wa manema labarai a ranar Litinin.
A cewar sanarwar, za a fara amfani da sabuwar fasahar ne ga daliban da za su zana jarrabawar kammala sakandare ta yammacin Afirka (WASSCE) masu zaman kansu a watan Fabrairun 2024, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ci gaba da cewa:
“A bisa tsare-tsare da ake amfani da su mafi kyawu a duniya, ofishin hukumar shirya jarabawar WAEC, na son sanar da jama’a, da duk masu ruwa da tsaki, cewa ta kammala shirin mayar da rubuta jarabawar WASSCE ga dalibai masu zaman kansu, daga takarda zuwa kwanfuta (CBT)."
Tsarin da ake amfani da shi yanzu
Tuni dai kowa ya sani hukumar shirya Jarrabawar shiga jami’a (JAMB), ta kawo canjin tsara gudanar da jarrabawar gama-gari da take yi duk shekara ga dalibai masu shiga jami'a (UTME), wato tsarin jarrabawar shiga manyan makarantun Najeriya, daga takarda zuwa tsarin CBT.
Haka ita ma hukumar WAEC ta sha yin tsokaci kan yanayin yadda ake zana jarabawarta, da kuma duba yiyuwar sabunta tsarin zuwa na zamani.
Hukumar mai shekaru 72 da kafuwa, ita ce hukumar da ta fi tsufa a yankin Afirka ta Yamma, kuma ta ci gaba da rike kambun girmamawarta yayin da makarantu na duniya ke karbar sakamakonta don bayar da gurbin karatu da sauran damammaki.
WAEC Ta Saki Sakamakon Jarabawar 2023 WASSCE
Hukumar shirya jarabawar kammala karatun sakandire ta West African Examinations Council (WAEC) ta bayyana sakin sakamakon jarabawar West African Senior School Certificate Examination (WASSCE) na shekarar 2023, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.
Asali: Legit.ng