Shugaba Tinubu da Mukarrabansa Sun Daura Haramar Yin Umrah a Ziyararsu Ta Saudiyya
- Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya kai ziyara kasar Saudiyya don halartar wasu tarukan zuba hannun jari
- Tinubu zai yi aikin Umrah tare da wasu jiga-jigan siyasar kasar nan da suka yi masa rakiya a ziyarar
- Wannan ne karo na biyu da shugaban kasa Tinubu ya kai ziyarar aiki wata kasar waje tun hawansa mulki
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
Kasar Saudiyya - Rahotanni sun bayyana cewa, shugaba Bola Tinubu zai yi Umrah jim kadan bayan kammala zamansa a Riyadh babban birnin kasar Saudiyya.
Aminiya Daily Trust ce ta ruwaito hakan a cikin wasu hotuna da ta yada a ranar Lahadi 12 ga watan Nuwamba, 2023.
Yakar Falasdinawa da Isra'ila ke yi: Ayarin farko na motocin agaji daga daular Saudiyya sun isa Gaza
A cikin hotunan, an ga shugaban tare da rakiyar gwamna Umar Bago na jihar Neja da wasu mutane uku.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalli hotunan a nan:
Abin da ya kai Tinubu Saudiyya
A baya dai shugaba Tinubu ya bayyana komai a shafinsa na X game da abin da ya kai shi kasar Larabawa, inda ya bayyana neman masu zuba jari tare da kulla yarjejeniya da gwamnatin Saudiyya a fannin sarrafa matatun man Najeriya.
Yace:
“Na bi sahun manyan gwamnati da shugabannin ‘yan kasuwa a yau a taron zuba jari na Saudiyya da Najeriya da aka yi a birnin Riyadh, tare da sako daga zuciyar Najeriya cewa: A shirye muke mu kawo sauyi, a shirye ga zuba jari, a shirye ga ci gaba, a shirye don kasuwanci.
“A matsayinmu na gwamnati, mun dauki matakai masu dorewa, tare da share fagen gudanar da harkokin kasuwanci cikin ‘yanci, tare da tabbatar da matsayinmu na yaki da cin hanci da rashawa.
“Ina kuma jaddada mahimmancin yawan matasanmu, matasan Najeriya abin alfaharinmu ne, a shirye suke su kara kirkiro sabbin abubuwa da kuma daukaka al’ummarmu a duniya."
Ga cikakken bayaninsa:
Yadda Tinubu ya ci kudi a taron UN
A wani labarin, kudin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta kashe a wajen halartar taron majalisar dinkin duniya kwanaki ya jawo surutu a gida.
Binciken jaridar FIJ ya nuna gwamnatin tarayya ta batar da $507,384 domin tawagar shugaban kasa ta kama dakuna kurum a dankareren otel.
Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya na cikin wadanda su ka je babban taron da majalisar dinkin duniya ta shirya a New York a Amurka.
Asali: Legit.ng