Sojin Saman Najeriya Sun Yi Ruwan Bama-Bamai Kan Motocin ’Yan Ta’adda a Borno
- An bayyana yadda sojojin Najeriya suka yi nasarar kashe 'yan ta'adda a wasu yankunan jihar Borno
- An lalata motocin bindiga mallakin 'yan ta'adda, da alamu an kashe da yawa a yayin da suke shirin kai hari
- Jihar Borno na daga jihohin da ke yawan fama da barnar 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP a shekaru da yawa
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
Jihar Borno - Rundunar sojin Operation Hadin Kai ta fatattaki ‘yan ta’adda da dama a yankin Ajigin da Banki na Borno a wasu hare-hare biyu da suka kai ta sama a ranakun 8 da 11 ga watan Nuwamba.
Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na rundunar sojojin saman Najeriya Edward Gabkwet ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito.
Yakar Falasdinawa da Isra'ila ke yi: Ayarin farko na motocin agaji daga daular Saudiyya sun isa Gaza
Ya bayyana cewa, ana ci gaba da gudanar da aikin kakkabe ragowar ‘yan ta’addan da ke boye a dazukun yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka gano motocin bindiga
Ya kara da cewa, ‘yan ta’addan sun boye manyan bindigogi guda hudu a karkashin ciyayi masu kauri da nufin kai mummunan farmaki kan sojin a kusa da Damboa da Wajiroko.
A cewarsa, an tabbatar da akwai motoci a wurin ne bayan da hayaki da wuta ta tashi bayan harba roka da sojojin suka yi, rahoton The Sun.
A wani harin kuma na ranar 11 ga watan Nuwamba, sojojin sun yi nasarar lallasa tsagerun 'yan ta'adda a magamar Banki ta Borno.
Barnar 'yan ta'adda a Banki
A cewar kakakin sojin, wurin da aka farmaki tsagerun ya yi kaurin suna wurin samun barnar 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP da ke addabar Arewa maso Gabas.
Ya kuma ce, 'yan ta'addan na amfani da wurin a matsayin mahadarsu ta harkalla da kuma wurin kisa kai munanan hare-hare kan jami'an tsaro.
Jihar Borno ne dai na daga cikin jihohin Arewacin Najeriya da ke fama da ta'addancin 'yan ISWAP da Boko Haram a tsawon lokaci.
An kai hari kan jami'an JTF
Wasu kwamandojin Civilian JTF guda biyu sun rasa rayukansu sakamakon fashewar wani bam da ake kyautata zaton na 'yan ta'addan Boko Haram ne a kusa da kauyen Ndufu da ke karamar hukumar Ngala a jihar Borno.
Majiyoyin tsaro da mutanen yankin sun bayyana cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe 10:00 na safiyar ranar Alhamis, 9 ga watan Nuwamba, cewar rahoton Daily Trust.
Asali: Legit.ng