Zaben Imo 2023: Fada Ya Barke Yayin da INEC Ta Fara Tattara Sakamakon Zabe
- Wasu 'yan siyasa da ba a san ko su waye ba, sun yi awon gaba da jami'an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), tare da wasu muhimman kayayyakin zabe
- Rahotanni sun bayyana cewa an fara samun matsala ne bayan da jami’an hukumar suka sanar da kuri'un da kowace jam’iyya ta samu a rumfar 015 da 016
- Wakilan jam'iyyun siyasa da ke wajen, su ka fara hatsaniya kan sanya sunayen a babban kundin rubuta sakamakon zabe, inda 'yan siyasar suka yi awon gaba da jami'an
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Imo - An samu hatsaniya a makarantar firamare ta garin Umuodu, Ezinihitte Mbieri, a karamar hukumar Mbaitoli ta jihar Imo.
A wurin ne ake tattara sakamakon zaben gwamnan jihar da ake yi, inda wasu ‘yan siyasa suka yi awon gaba da jami’an zabe da takardun rubuta sakamakon zabe.
Wakilinmu wanda ya bi diddigin lamarin, ya lura cewa an fara samun matsala ne bayan da jami’an hukumar zabe ta INEC, suka sanar da kuri'un da kowace jam’iyya ta samu a rumfar 015 da 016, ba tare da sun shigar da hakan a cikin takardar sakamakon zaben ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A rumfar 016, jami'in INEC ya fadi sakamako kamar haka:
LP - 19
APC - 21
PDP - 16
ADP - 2
AA - 1
Sai dai an bukaci jami’an da kada su shigar da sakamakon zaben a cikin takardar tattara sakamakon zaben, suka ki, lamarin da ya haifar da fada tsakanin jam’iyyun APC, LP, da PDP.
A yayin da ake ci gaba da hatsaniyar, wasu ‘yan siyasa da ake kyautata zaton ‘ya’yan jam’iyyar APC mai mulki ne a jihar, su ka yi awon gaba da jami’an hukumar zaben tare da kayan zaben da suka hada da takardar rubuta sakamakon zaben.
An yi arangama tsakanin 'yan sanda ta wakilan jam'iyya
A wani labarin daga jihar Imo, kun ji cewa; hankalin jama'a ya tashi a yayin da jami’an ‘yan sanda suka yi arangama da wakilan jam’iyya, a makarantar Amaimo Central, gundumar Amaimo, karamar hukumar Ikeduru ta jihar.
TheCable ta ruwaito cewa, rikicin ya fara ne lokacin da wasu wakilan jam’iyya suka dage da cewa kada jami’an ‘yan sanda su raka jami’an hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) zuwa daya daga cikin rumfunan zabe da ke unguwar.
An ce jami’an ‘yan sandan sun dage akan sai sun raka jami’an INEC tare da kayyakin zabe zuwa rumfar zaben, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.
Asali: Legit.ng