Zaben Gwamnan Imo 2023: Jam’iyyar PDP Ta Ci Zabe a Akwatin Farko Da Aka Bayyana Sakamako

Zaben Gwamnan Imo 2023: Jam’iyyar PDP Ta Ci Zabe a Akwatin Farko Da Aka Bayyana Sakamako

  • Rahotannin da ke shigo mana na nuni da cewa, jam'iyyar PDP ta samu kuri'u mafi rinjaye a akwatin makarantar 'Community' da ke Obodo, jihar Imo
  • Kamar yadda sakamakon ya nuna, PDP ta samu kuri’u 77, yayin da APC, ta samu kuri’u 17, sai kuma Labour ta samu kuri’u hudu.
  • Tun da farko, Samuel Anynawu, dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, ya ce yana fatan samun nasara idan har aka gudanar da sahihin zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ikeduru, Jihar Imo - Jam’iyyar PDP ta samu nasara a makarantar Community, Obodo, unguwar Araimo, a karamar hukumar Ikeduru ta jihar Imo.

Jam’iyyar PDP ta samu nasara a akwatin zaben makarantar 'Community' da ke Obodo, gundumar Araimo, a karamar hukumar Ikeduru ta jihar Imo.

Kara karanta wannan

Labari Mai Zafi: DSS da EFCC Sun Dura Rumfar da Dino Melaye Zai Dangwala Kuri’a

Samuel Anyanwu
Tun da fari, dan takarar PDP, Samuel Anyanwu, ya yi hasashen samun nasara a zaben Hoto: Senator Samuel Anyanwu
Asali: Facebook

Jam’iyyar ta samu kuri’u 77, inda ta doke jam’iyyar All Progressives Congress (APC), wadda ta biyo bayanta da kuri’u 17 yayin da Labour ta samu kuri’u hudu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun da farko, a lokacin da ya kada kuri’arsa a rumfar zabe mai lamba 012, da ke makarantar firamare ta garin Ama Imo da ke karamar hukumar Ikeduru, Samuel Anynawu, dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, ya ce yana fatan samun nasara.

Ni ne zan yi nasara - Dan takarar PDP

Yace idan zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali, tabbas zai samu nasara a karshe.

Dan takarar ya ce:

“Gaskiya komai ya fara lafawa yanzu, a gundumomi bakwai, an kwashe akwatunan zabe, amma na san hakan ba zai hana ni yin nasara ba."
“INEC ta ce ba za ta kidaya kuri’u a duk inda aka samu tashin hankali ba. Idan zabe ya kasance sahihu wanda babu magudi, to na san ni zan ci zabe."

Kara karanta wannan

"15k daga APC, PDP na biyan 13k", Ana zargin siyan kuri'a a Bayelsa, Bayanai sun fito

“Ban damu da sace kuri’u ba, saboda INEC ta ce duk wuraren da aka samu tashin hankali ba za a kirga kuri'unsu ba.”

Wanene Samuel Anyanwu? Dan takarar gwamnan PDP a jihar Imo

Sanata Samuel Anyanwu, ya kasance fitaccen jigo ne a siyasar Najeriya, wanda ya shahara wajen jajircewa kan yi wa al’umma hidima da kuma bayar da gudunmawa wajen ci gaban jama'arsa.

Gudunmawar da ya bayar a fagen siyasa da na taimakon jama’a, na nuni da yadda ya ke da himma wajen inganta rayuwar al’ummar da ya ke wakilta, wanda hakan ya sa ya yi fice a fagen siyasar Najeriya, musamman a jihar da ya fito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.