Masarautar Bauchi Ta Tsige Masu Rike da Sarauta 6, Ta Ɗauki Mataki Mai Tsauri Kan Hakimi
- Masarautar Bauchi ta tsige rawanin da aka naɗa wa sabbin masu riƙe da sarautar gargajiya shida a yankin Galambi
- A wata sanarwa da masarautar da fitar, ta ce Hakimin Galambi ya saɓa wa doka da ƙa'idoji wajen naɗin sarauta
- Ta kuma ɗauki matakin haramta wa hakimin naɗin sarauta na tsawon shekara ɗaya, wanda zai fara daga ranar 7 ga watan Nuwamba
Ahmad Yusuf, kwararren Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Bauchi - Majalisar Masarautar Bauchi ta tsige wasu sabbin masu rike da sarautar gargajiya guda shida a yankin Galambi da ke ƙarƙashin masarautar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wannan matakin na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun Masarautar, Babangida Hassan Jahun, ya fitar.
Ya yi bayanin cewa an ɗauki wannan matakin ne bisa la'akari da matakan da hakimin Galambi, ya bi wajen naɗa wa mutanen Sarauta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sanarwan, matakan da aka gano hakimin ya bi, sun saɓa wa doka da ƙa'idojin naɗin irin waɗannan Sarautar gargajiyan, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
An tattaro cewa Hakimin, Alhaji Shehu Adamu Jumba wanda ke rike da sarautar Danlawal na Masarautar Bauchi, ya bai wa wasu mutane shida sarauta a fadarsa kwanakin baya.
Sarautar gargajiyar da ya naɗa wa mutanen su ne, Galadaman Danlawal, Wakilin Dokan Danlawal, Majidadin Danlawal, Wakilin Gonan Danlawal, Sarkin Dajin Danlawal da kuma Hardon Danlawal.
Masarautar Bauchi ta ɗauki mataki kan hakimin
Bugu da ƙari, Sanarwan ta kara da bayanin cewa Masarautar Bauchi ta haramta wa Hakimin yin kowane irin naɗin sarauta na tsawon shekara ɗaya wanda zai fara daga ranar 7 ga watan Nuwamba, 2023.
"Ya zama wajibi a ko da yaushe ya tabbatar da cewa duk wani mataki na naɗin Sarauta dole ne ya kasance ya yi daidai da doka da ka'idojin cikin masarautar," in ji sanarwan.
Ɗan majalisar LP ya yi nasara a Kotun ɗaukaka ƙara
A wani rahoton kuma Bayan Kotun zaɓe ta soke nasararsa, ɗan majalisar tarayya na LP daga Legas ya samu nasara a Kotun ɗaukaka ƙara.
Kotun ta jingine hukuncin farko, kana ta tabbatar da Thaddeus Attah a matsayin sahihin ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Eti Osa a Legas.
Asali: Legit.ng