"Gagarumin Magudi a Dukkan Rumfunan Zaben Kogi" Dino Melaye Ya Zargi APC Da Magudin Zabe
- Dino Melaye, ya umurci jami'an jam'iyyarsu da su nuna turjiya idan INEC ta ki nuna masu tsaftatacciyar takardar rubuta sakamakon zabe
- Melaye, dan takarar gwamnan jihar Imo, ya yi zargin cewa jami'an hukumar zaben sun ki nuna wa jami'ansu takaradar rubuta sakamakon zaben don tantance wa
- Ya ce an dakatar da kada kuri'a a Ogori Mangogo, inda lamarin ya faru, har sai jami'an hukumar sun nuna wa jami'ansu takarar, ko su tayar da zanga-zanga
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Lokoja, jihar Kogi – Dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Kogi, Sanata Dino Melaye, ya shaida wa wakilan jam’iyyarsa da su yi turjiya tare da yin zanga-zanga matukar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ki nuna masu tsaftatacciyar takardar rubuta sakamakon zabe.
Melaye, ya ce ba a fara kada kuri’a a Ogori Mangogo ba, saboda ma’aikatan INEC sun ki nuna takardar rubuta sakamakon zabe ga wakilan PDP.
Tsohon dan majalisar, ya bayyana hakan a shafin na X (wanda aka fi sani da Twitter) @_dinomelaye, a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“An dakatar da kada kuri’a a mazabar ogori mangogo, saboda jami'an INEC sun ki nuna wa wakilanmu tsaftatattun takardun rubuta sakamakon zabe. Idan sun ki nuna muku sahihan takardun sakamakon zaben, ku yi turjiya da zanga-zanga."
Wanda zai lashe zaben Kogi - Hasashen 'yan Najeriya
Gabanin zaben jihar Kogi, yan Najeriya a shafukan sada zumunta sun yi hasashen wanda zai yi nasara a zaɓen jin ra'ayi da Legit.ng ta gudanar a shafin Twitter.
Bayanai na INEC sun nuna cewa jam’iyyun siyasa da yan takara 18 ne ke fafatawa a zazen, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.
A zaben jin ra'ayin da Legit.ng ta gudanar a shafin Twitter, 54.4% na wadanda suka yi zaben sun ce Dino Melaye, dan takarar jam'iyyar PDP ne zai lashe zaben, yayin da 26% suka zabi Usman Ahmed Ododo na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Asali: Legit.ng