Dakarun Soji Sun Damke Wasu Motoci 3 da Ake Zargi a Zaben Jihar Kogi

Dakarun Soji Sun Damke Wasu Motoci 3 da Ake Zargi a Zaben Jihar Kogi

  • Jami'an rundunar soji da ke aikin zabe a jihar Kogi sun cafke wasu motoci uku a ranar zabe
  • Haka kuma, sojojin sun kama gaba daya mutanen da ke cikin motocin wadanda basu yarda da su ba
  • A yau Asabar, 11 ga watan Nuwamba ne al'ummar jihar Kogi za su zabi sabon gwamna na zai jagorance su na tsawon shekaru hudu

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kogi, Lokoja - Zaben gwamnan jihar Kogi yana da matukar muhimmanci ga al'ummar jihar Kogi masu karamci yayin da mutane suka fara tururuwar fita don sauke hakokinsu, kamar yadda Legit Hausa take bibiya a Arise TV a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.

Sojoji sun kama motoci a Kogi
Da Duminsa: Sojoji Sun Cafke Wasu Motoci 3, Sun Kama Mutanen Ciki Yayin da Al’ummar Kogi Ke Zabe Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Sai dai a wani yanayi na daban, tawagar rundunar soji na musamman da ke aikin zabe a jihar, ta kama wasu bakaken motocin tsaro guda uku da ba a san daga ina ba, rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

An sace jami'in INEC, takardar sakamakon zabe sun ɓace a hatsarin jirgin ruwa a Bayelsa

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, jami'an sojojin sun kama motocin ne a safiyar ranar Asabar a mararrabar Itakpe, hanyarsu ta zuwa yankin Okene da ke jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An takaita zirga-zirga a jihar Kogi yayin da sojoji suka cafke motoci da mutanen ciki

Akwai dokar hana zirga-zirgar ababen hawa a jihar daga karfe 12:00 na daren ranar Juma'a, 10 ga watan Nuwamba zuwa karfe 6:00 na yammacin ranar Asabar, yayin da masu kada kuri'a ke zaben sabon gwamna a yau.

Rundunar sojin ta zargi motocin guda uku da mutanen da ke ciki sannan ta kama su nan take.

Zaben Bayelsa: An bankado jami'an tsaro na bogi

A gefe guda, rundunar yan sandan ta bayyana aniyar ta na fatattakar jami’an tsaron bogi da yan siyasa suka baza domin kawo cikas a zaben gwamnan Bayelsa a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.

Daniel Sokari-Pedro, Mataimakin Sufeto Janar na yan sanda (DIG) mai kula da Kudu-maso-kudu, ya bayyana wa manema labarai a Yenagoa a ranar Juma’a, 10 ga Nuwamba, cewa yan sanda za su yi taka-tsantsan wajen zakulo wadannan jami’an tsaro na bogi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng