"Sun Yi Sakaci Kan Batun Tsaro" Matawalle Ya Tabo Gwamnatin Buhari Kan Matsalar Tsaro
- Bello Matawalle ya bayyana cewa tsohuwar gwamnatin da ta shuɗe ba ta ɗauki batun tsaro da muhimmancin da ya kamata ba
- Karamin Ministan tsaro kuma tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ya ce ma'aikatar su ta kawo sabbin jiragen yaƙin domin kawo karshen lamarin
- Ya yi wannan bayani ne yayin da ya bayyana a gaban kwamitin tsaro na majalisar dattawa a Abuja
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Karamin ministan tsaron Najeriya, Bello Matawalle, ya ce gwamnatin da ta gabata ba ta dauki batun rashin tsaron ƙasar nan da muhimmanci ba.
Matawalle, tsohon Gwamnan jihar Zamfara ya faɗi haka ne yayin da ya bayyana gaban kwamitin tsaro na majalisar dattawa tare da Ministan tsaro, Abubakar Badaru.
Ƙaramin Ministan ya faɗa wa kwamitin cewa ba da daɗewa ba ma'aikatar tsaro ta karɓi sabbin jiragen yaƙi masu saukar Angulu domin haɓaka yaƙi da ƴan ta'adda.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matawalle ya kuma bayyana cewa sha'anin tsaro abu ne mai muhimmanci wanda ke bukatar haɗin guiwa da maida hankali daga gwamnatin tarayya, jiha da karamar hukuma.
An yi sakaci a baya - Matawalle
A kalamansa, ƙaramin Ministan tsaro Matawalle ya ce:
“A matsayina na tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, na san halin da na shiga kan matsalar tsaro, musamman ‘yan bindiga wanda sabon abu ne a gare mu a yankin Arewa maso Yamma."
"Batun Boko Haram ba sabon abu ba ne a yankin Arewa maso Gabas, amma duba da abin da ya faru a gwamnatin da ta gabata, ko kaɗan ba a dauki batun da muhimmanci ba."
“A yau muna daukar matakai don magance irin wadannan masu aikata laifuka. Batun tsaro na bukatar hadin kai daga jihohi, kananan hukumomi da gwamnatin tarayya."
Matawalle ya kara da cewa Najeriya na buƙatar muhimman dokoki daga ɓangaren majalisun tarayya domin kawo ƙarshen duk wani kalubalen tsaro, Vanguard ta ruwaito.
Dakarun sojoji sun bankaɗo wani makirci da aka ƙulla
A wani rahoton na daban Rundunar soji ta sake sabon gargaɗi bayan gano wasu gurɓatattu na shirin yin shigar sojoji a zaɓen gwamna da ke tafe a jihohi uku.
Kakakin rundunar, Edward Buba, ya ce dakaru sun shirya raunata duk wanda ya yi yunkurin tada zaune tsaye lokacin zaɓen.
Asali: Legit.ng