'Yan Bindiga Sun Shiga Uku, Gwamnan Arewa Na PDP Ya Aike da Buƙata 1 Ga Hukumomin Tsaron Jiharsa

'Yan Bindiga Sun Shiga Uku, Gwamnan Arewa Na PDP Ya Aike da Buƙata 1 Ga Hukumomin Tsaron Jiharsa

  • Dauda Lawal ya yi kira ga hukumomin tsaro su ƙara danƙon hadin kai a tsakanin su domin tabbatar da tsaro a Zamfara
  • Gwamnan ya bayyana cewa tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma ne babban abin da ya sa gaba a gwamnatinsa
  • Ya yi wannan kira ne a taron majalisar tsaron jihar Zamfara wanda ya gudana ranar Alhamis a gidan gwamnatin Gusau

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara - Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara, a ranar Alhamis, ya buƙaci ƙara danƙon hadin gwiwa da aiki tare a tsakanin hukumomin tsaro a jihar da ke Arewa maso Yamma.

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara.
Zamfara: Gwamna Lawal Ya Bukaci Hukumomin Tsaro Su Yi Aiki Tare Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Lawal ya yi wannan kira ne yayin da yake jagorantar taron majalisar tsaron jihar Zamfara a gidan gwamnati da ke Gusau, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

Abin da ya faru bayan an sace daliban Jami'ar Zamfara – Matawalle ya magantu

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar bayan kammala taron ranar Alhamis, 9 ga watan Nuwamba, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bugu da kari, Gwamnan ya jaddada bukatar da ke akwai na jami’an tsaro su ƙara hada kai tare da musayar bayanan sirri domin haɓaka aikinsu wajen yakar ‘yan bindigan jeji.

Sanarwan ta ce:

"A wurin taron majalisar tsaron jihar Zamfara da aka yi yau, Gwamna Dauda Lawal ya jagoranci tattaunawa kan yadda za a kawo ƙarshen ƴan bindiga da sauran muggan laifuka."
"Ya sanar da mambobin kwamitin tsaro cewa an kammala zabar mambobin kwamitin kafa rundunar ƴan sa kai 'Community Protection Guards’ a kananan hukumomi 14 na jihar."
"A ƙarshen makon nan za a fara baiwa jami'an rundunar horo. Gwamnan ya bukaci shugabannin hukumomin tsaro da su kara matsa ƙaimi a sintiri saboda rahotan ‘yan bindiga da ke kwararowa daga jihohin makwabta.”

Kara karanta wannan

Kogi: "Ni ake nema a kashe" Ɗan takarar Gwamna ya tona shirin Gwamnan APC a jihar arewa

Lawal ya ƙara nanata cewa tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma shi ne babban abin da gwamnatinsa ta sa a gaba.

Ya kuma bayyana cewa a koda yaushe a shirye yake ya baiwa jami’an tsaro isassun kayan aiki da goyon baya don taimaka musu wajen cimma wannan manufa.

Yan bindiga sun sake kai hari a jihar Sakkwato

A wani rahoton kuma Yan bindiga sun kai mummunan hari kan ƙauyuka biyu a karamar hukumar Rabbah a jihar Sakkwato, sun halaka mutane.

Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun kai hare-haren lokuta daban daban, sun sace dabbobi tare da ƙona gidaje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262