A Karshe, An Bayyana Halin da Tsohon Gwamnan Babban Banki CBN Ya Shiga Bayan Hukuncin Kotu

A Karshe, An Bayyana Halin da Tsohon Gwamnan Babban Banki CBN Ya Shiga Bayan Hukuncin Kotu

  • Daga karshe bayan hukuncin Kotu, tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya shaki iskar ƴanci
  • Wannan ya biyo bayan belin da ya samu a babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja, babban lauyansa ya tabbatar da haka
  • An kama Emefiele a washe garin ranar da shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya dakatar da shi daga matsayin gwamnan CBN

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele, ya shaƙi iskar ƴanci bayan shafe watanni biyar a tsare kan zargin cin hanci.

Tsohon gwamnan babban banki CBN, Godwin Emefiele.
Tsohon Gwamnan CBN Ya Shaki Iskar Yanci Bayan Watanni 5 a Tsare Hoto: Mr Godwin Emefiele
Asali: UGC

Ɗaya daga cikin manyan lauyoyin da suka tsayawa Emefiele a Kotu ne ya tabbatar da sakinsa ga jaridar Premium Times ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Emefiele: Kotu ta cimma matsaya kan tsohon gwamnan CBN bayan mika shi da EFCC ta yi

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin kasa zagon ƙasa (EFCC) ta saki Emefiele ne biyo bayan hukuncin da babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja ta yanke ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ta amince da ba da belin tsohon Gwamnan CBN ɗin a zamanta na jiya bayan EFCC ta bi umarni, ta gurfanar da shi a gabanta.

Da yake tabbatar da sakin Emefiele ranar Alhamis, ɗaya daga cikin lauyoyinsa, Matthew Burkaa (SAN), ya ce wanda yake karewa ya sami damar tafiya gida daga Kotu a jiya Laraba.

"Kotu ta sake shi kuma an damƙa mana (lauyoyinsa) shi a jiya, tare muka bar harabar Kotu da shi (tsohon Gwamnan CBN)," in ji Burkaa.

Yadda Emefiele ya sha ankwa

Hukumar tsaron farin kaya (SSS) ta kama Mista Emefiele a ranar 10 ga watan Yuni, washe garin da aka dakatar da shi daga matsayin gwamnan CBN, kuma tun wannan lokaci yake tsare.

Kara karanta wannan

Kogi: "Ni ake nema a kashe" Ɗan takarar Gwamna ya tona shirin Gwamnan APC a jihar arewa

A baya-bayan nan a watan Oktoban da ya gabata, hukumar SSS ta miƙa shi ga EFCC, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Duk da cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya kayyade wa’adin tsare wanda ake zargi mafi yawa sa’o’i 48, amma doka ta bai wa jami’an tsaro damar tsawaita lokacin bisa izinin kotu.

Hukumar SSS dai ta yi ikirarin cewa ta samu umarnin kotu na tsawaita tsare shi, kafin daga bisani ta mika shi ga hukumar EFCC domin ci gaba da binciken shari’ar da ake yi masa.

Kotun Ɗaukaka Kara Ta Tsige Ƴan Majalisar Tarayya 3

A wani rahoton kuma Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin korar ƴan majalisun tarayya na PDP uku daga majalisar wakilan tarayya.

Yayin yanke hukunci ranar Talata, Kotun mai zama a Abuja ta ce PDP ta saɓa umarnin Kotu, don haka duk ƙuri'un da ta samu basu da amfani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262