Zaben Gwamnan Bayelsa: Abin Da Ya Sa Zan Samu Nasarar Zarcewa – Gwamna Diri Ya Yi Bayani
- Gwamnan jihar Bayelsa mai ci a yanzu, Douye Diri, ya ce yana da tabbacin al'umar jihar Bayelsa za su sake zabensa karo na biyu a zaben jihar da ke zuwa
- Gwamna Diri, ya yi nuni da cewa ba wata tsiya da abokin karawarsa na APC ya yi a lokacin da ya ke gwamnan jiha, don haka ba ya kallonsa matsayin barazana
- Ya kuma ce gwamnatinsa ta shafe shekaru hudu a kan gadon mulki, kuma tana aiwatar da ayyukan da ta gada da kuma sabbin da ta kaddamar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Bayelsa - Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri, yana da yakinin cewa jama'a za su sake zabar shi a karo na biyu, bisa ayyukan da ya shimfida a jihar, a wa'adin mulkinsa na farko.
Da yake jawabi ga dimbin jama’a a babban taron yakin neman zabensa na karshe da aka gudanar a 'Oxbow Lake Pavilion' a Yenagoa, a ranar Talata, Gwamna Diri ya ce gwamnatinsa ta kammala ayyukan da ya gada sannan kuma ta gudanar da nasa ayyukan.
Sai dai abokin hamayyarsa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya kira gwamnatin Diri da gwamnatin da mutane ke shan wahalarta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ayyukan da na shimfida a jihar Bayelsa - Gwamna Diri
Gwamna Diri ya ce:
“Sun ce ayyukan da muka gada kawai muka kammala. Amma gadar Unity da ke Nembe, inda abokin hamayyata na APC ya fito kuma ya yi watsi da ita, an gina ne a karkashin gwamnatina, kuma aikin ya kammala."
“A yau, daya daga cikin mafi kyawun titin aben hawa mai hannu biyu a Yenagoa, wato 'Glory Drive', wanda suka karbi biliyoyin kudi don gina wa amma suka yi watsi da shi, gwamnatina ta kammala kuma ta kaddamar da shi.”
Diri, ya bayyana cewa dan takarar jam’iyyar APC, Timipre Sylva, ya yi gwamna na tsawon shekaru biyar, amma bai yi wani aikin azo a gani da zai iya yin yakin neman zabe ba da shi ba, illa amfani da karairayi kawai.
Gwamna Diri ya abin alfahari ne ga al'umarsa - Gwamna Kefas
Ya kuma ce gwamnatinsa ta shafe kimanin shekaru hudu a kan gadon mulki, kuma tana aiwatar da ayyukan da ta gada da kuma sabbin da ta kaddamar.
Shugaban jam’iyyar PDP na majalisar yakin neman zaben gwamnan Bayelsa, Dr. Agbu Kefas, wanda kuma shi ne gwamnan jihar Taraba, ya bayyana Diri a matsayin alamar zaman lafiya, ci gaba da kuma abin alfahari ga al'umarsa.
Gwamna Kefas ya ce ayyukan takwaransa na Bayelsa da shirye-shiryensa, sun nuna cewa ya damu da walwala da jin dadin jama'arsa.
Gwamna Diri ya shiga matsala Ana dab da zaben Bayelsa
A wani labarin, kunji cewa an shigar da wata sabuwar kara ta neman soke takarar Gwamna Douye Diri da mataimakinsa, Lawrence Ewhrudjakpo, a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, kasa da kwanaki a gudanar da zaben gwamnan jihar Bayelsa
Karar dai ta nemi umarnin tilasta hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da ta cire sunayen Diri da Ewhrudjakpo a matsayin yan takarar jam'iyyar PDP a zaɓen ranar 11 ga watan Nuwamba, cewar rahoton Premium Times.
Asali: Legit.ng