Kungiyar Yarbawa ta Afenifere Ta Caccaki Hukuncin Kotun Koli da Nasarar Tinubu

Kungiyar Yarbawa ta Afenifere Ta Caccaki Hukuncin Kotun Koli da Nasarar Tinubu

  • Hukuncin kotun ƙoli bai yi wa wasu ƴan Najeriya daɗi ba, inda suka fara fitowa suna sukar sa a fili
  • Shugaban ƙungiyar Afenifere, Pa Ayo Adebanjo ya yi fatali da hukuncin da kotun ƙoli ta yanke wanda ya tabbatar da nasarar zaɓen Bola Tinubu
  • Ƙungiyar ta Yarbawa ta bayyana cewa garambawul ɗin da aka yi wa dokar zaɓe baya da wani amfani

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jagoran ƙungiyar Afenifere, ƙungiyar siyasa da zamantakewar al'ummar Yarabawa, ta yi Allah-wadai da hukuncin da kotun ƙoli ta yanke, wanda ya tabbatar da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen da aka yi na ranar 25, ga watan Fabrairu.

Afenifere ta caccaki hukuncin kotun koli
Kungiyar ta caccaki hukuncin da kotun koli ta yanke Hoto: Pa Ayo Adebanjo, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Pa Ayo Adebanjo ya caccaki hukuncin kotun ƙoli

Afenifere a ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Ayo Adebanjo ya fitar, a ranar Talata, 7 ga watan Nuwamba, makonni biyu bayan kotun ƙoli ta tabbatar da nasarar da Tinubu ya samu a zaɓen, a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Kara karanta wannan

"Yana Tunanin Waye Shi?": Ƴan 'Obidients' sun koma caccakar Peter Obi Kan Wani Abu 1

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ƙungiyar Pa Adebanjo ya ce sauye-sauyen da aka yi kan dokar zaɓe, bayan ƴan Najeriya sun buƙaci hakan, da biliyoyin kuɗin da aka kashe wajen gudanar da zaɓen 2023, asara kawai aka yi saboda hukuncin kotun ƙolin, cewar rahoton The Cable.

Ƙungiyar ta kuma caccaki siyo motocin alfarma ƙirar SUV waɗanda kuɗinsu sun kai N160m ga ƴan majalisar wakilai da sanatoci, rahoton New Telegraph ya tabbatar.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Ƙungiyar Afenifere ta lura cikin takaici hukuncin da kotun koli ta yanke na baya-bayan nan, wanda ya amince da fashin da aka yi musamman a zaɓen shugaban ƙasa."

APC Ta Aikawa Atiku, Obi Sako Kan Hukuncin Kotun Koli

A wani labarin kuma, jam'iyyar All Progressuves Congress (APC) ta aika saƙo ga Atiku Abubakar da Peter Obi kan hukuncin kotun ƙoli.

Jam'iyyar ta buƙaci manyan ƴan takarar biyu da su mayar da takkubansu su yi sansanci da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng