Shugaba Tinubu da Ministoci 5 Sun Shilla Zuwa Kasar Waje, An Bayyana Inda Suka Je
- A ranar Alhamis shugaban ƙasa Bola Tinubu zai bar Najeriya, domin halartar wani muhimmin taro
- Tinubu zai halarci taron Saudiyya da nahiyar Afirka, wanda aka shirya gudanarwa a Riyadh ranar Juma’a 10 ga Nuwamba, 2023
- Bayo Onanuga ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a daren Laraba, 8 ga watan Nuwamba, inda ya ƙara da cewa Tinubu zai samu rakiyar manyan ministoci da sauran jami’an gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja zuwa birnin Riyadh, na ƙasar Saudiyya a ranar Alhamis, 9 ga watan Nuwamba, 2023.
Ana sa ran shugaban zai halarci taron Saudiyya da nahiyar Afirika, wanda aka shirya gudanarwa a birnin Riyadh, a ranar Juma’a 10 ga watan Nuwamba, 2023.
An bayyana abin da Tinubu zai yi a Saudiyya
Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai ba da shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabaru, ga Shugaba Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sanarwar da aka sanya a shafin X na Onanuga, Tinubu, a taron Saudiyya da Afirika, zai jaddada aniyar Najeriya na ƙara jawo masu zuba hannun jari ƴan ƙasashen waje kai tsaye da kuma faɗaɗa hulɗar kasuwanci.
Shugaban zai samu rakiyar:
1. Ministan harkokin jaje, Amb. Yusuf Tuggar
2. Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman
3. Ministan kuɗi da tattalin arziƙi, Wale Edun
4. Ministar harkokin agaji da rage Talauci, Dr Betta Edu
5. Ministan kasafin kuɗi da tsara tattalin arziƙi, Sen. Abubakar Bagudu.
Sauran su ne:
1. Mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Mallam Nuhu Ribadu
2. Darakta Janar na hukumar leƙen asiri ta ƙasa (NIA), Amb. Ahmed Rufa'i Abubakar
3.Shugaban hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON), Mallam Jalal Arabi.
Ana sa ran shugaban zai dawo ƙasar nan bayan kammala taron Saudiyya da nahiyar Afirika.
Tinubu Ya Yi Sabbin Nade-Nade
A wani labarin kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa sabbin kwamishinoni 20 a hukumar ƙidaya ta ƙasa (NPC).
Shugaban kasar ya bukaci sabbin kwamishinonin da su yi nasarar aiwatar da dukkan matakan da gwamnatinsa ta dauka don samar da ainihin bayanan jama'a.
Asali: Legit.ng