CBN Ya Fitar Da Sanarwa Kan Wa'adin Karbar Tsoffin Takardun Kudade
- Babban Bankin CBN ya tabbatar da cewa har yanzu tsoffin kudade halastattu ne kuma bai kamata aki karba ba
- CBN ya bayyana haka ne yayin da ake jita-jitar cewa babu isassun kudade a kasar da kuma hana karbar tsoffin kudade
- Bankin ya bayyana haka ne ta bakin daraktan yada labarai, Isa AbdulMumin a yau Laraba 8 ga watan Nuwamba
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Babban Bankin Najeriya, CBN ya bayyana cewa za a ci gaba da amfani da tsoffin kudade a kasar.
Bankin ya bayyana haka ne ta bakin daraktan yada labarai, Isa AbdulMumin a yau Laraba 8 ga watan Nuwamba, Daily Trust ta tattaro.
Wane korafi jama'a ke yi kan kudaden?
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da korafin karancin kudade a kasar, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, bankin ya musanta cewa akwai karancin kudin inda ya ce akwai makudan kudade da za su isa juya harkar kasuwanci.
Sanarwar ta ce:
"Saboda gudun kokwanto, mu na da isassun kudade da za a yi harkokin kasuwanci da su.
"Mu na sanar da ku cewa duk wani kudi da aka ba ku halastacce ne, bai kamata ku ki karba ba."
Bankin ya bai wa sauran bankuna umarnin ci gaba da bayar da sabbi da tsoffin kudade a kasar, cewar Vanguard.
Hausa Legit ta ji ta bakin wasu kan wannan lamari:
Umar Isa ya ce:
"Ni ba na ma tuna akwai tsoffin kudade sai da wadannan mutane su ka tunomin da su, saboda ni dukkansu kashe su nake yi.
Abdulhamid Dahiru ya ce Alhamdulillah gaskiya na ji dadin haka saboda irin bakar wahala da mu ka sha a baya.
CBN ya bayyana dalilin karancin kudade a kasar
A wani labarin, Babban Bankin Najeriya, CBN ya bayyana dalilan da su ka sanya karancin kudade a kasar.
Bankin ya ce mutane sun tsorata ne su ka fara cire makudan kudade saboda jita-jitar da ake cewa za a samu matsalar kudaden.
Wannan na zuwa ne yayin da aka fara tunanin bankin na shirin sa ka dokar kin karbar tsoffin kudade da wa'adinsu ya zo karshe.
Asali: Legit.ng