'Idan Ba Ki Ba Ni Hadin Kai Ba, a Ranar Aurenki Za Ki Mutu, Malamin Addini Ya Yi Barazana Ga Budurwa

'Idan Ba Ki Ba Ni Hadin Kai Ba, a Ranar Aurenki Za Ki Mutu, Malamin Addini Ya Yi Barazana Ga Budurwa

  • Jami’an ‘yan sanda sun kama wani Fasto kan zargin garkuwa da mutane da kuma lalata budurwa da aka ba shi jinya
  • Wanda ake zargin mai suna Sunday ya yi garkuwa da budurwar ce tare da mata barazanar za ta mutu a ranar aurenta idan ba ta amince ba
  • Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Omolola Odutola ta ce wanda ake zargin ya tabbatar da aikta laifukan kuma zai fuskanci hukunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ogun – Rundunar ‘yan sanda a jihar Ogun ta cafke shahararren Fasto kan zargin garkuwa da budurwa tare da lalata da ita.

Faston mai suna Sunday da ke cocin Cherubim a yankin Agbado da ke jihar Ogun ya shiga hannu bayan samun bayanai daga jama’a, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Mai magani ya dirkawa wani harsashi har lahira yayin gwada maganin bindiga a Bauchi

Fasto ya yi garkuwa da budurwa, ya lalata rayuwarta
Fasto ya yi barazana ga budurwa, ya lalata ta. Hoto: NPF.
Asali: Twitter

Mene ake zargin Faston a Ogun?

‘Yan sanda sun tabbatar da hakan inda su ka ce wacce aka yi garkuwan da ita ta je duba ‘yar uwarta ne da ba ta da lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Faston ya bayyana mata cewa ‘yar uwar tata mutuwa za ta yi a ranar aurenta idan har bai sadu da ita ba.

Faston ya kara da cewa duk wani wanda ya yi soyayya ko ya sadu da budurwar tabbas zai mutu idan dai ba shi ba ne.

Har ila yau, ‘yan sanda na zargin Faston da garkuwa da budurwar a ranar 2 ga watan Faburairu na wanna shekara, Gistlover ta tattaro.

Ta yaya abin ya faru a Ogun?

Dan uwan mahaifin yarinyar, Aliu Yusuf ya bayyana wa ‘yan sanda yadda Faston ya dauki Blessing na tsawon watanni tara su na tare.

Kara karanta wannan

Kano: Hisbah ta yi martani kan aske kan wata budurwa da kwalba, ta fadi matakin da ta dauka a kai

Ya ce Blessing ta bayyana mu su cewa Faston ya dauke ta zuwa gidansu inda daga nan su ka wuce otal tare da kwanciya da ita lokuta da dama.

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Omolola Odutola ta ce wanda ake zargin ya tabbatar da aikata laifukan kuma zai fuskanci hukunci.

Odutola ta kara da cewa an dauki wacce abin ya faru da ita zuwa asibiti bayan fahimtar ta samu matsalar kwakwalwa.

Yan sanda sun kama Fasto da kokon kan mutum

Kun ji cewa, jami’an ‘yan sanda sun kama wani Fasto da wasu mutane 3 da kokon kan dan Adam a jihar Ogun.

An tasa keyar Faston mai suna Oyenekan Oluwaseyi zuwa ofishin ‘yan sanda a ranar Asabar 14 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.