Gwamna Namadi na Jigawa Ya Dauki Wani Gingimemen Mukami Ya Ba Mace
- Gwamna Umar Namadi ya kafa tarihi a jihar Jigawa yayin da ya sanar da yin naɗin sabbin muƙamai a gwamnatinsa
- Gwamnan ya ɗauko Zainab Shu'aibu Rabo Ringim ya ba ta muƙamin babbar mataimakiyarsa ta musamman kan harkokin yaɗa labarai
- Zainab Ringim ita ce mace ta farko tun bayan da aka kafa jihar Jigawa a shekarar 1991 da ta samu wannan muƙamin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi
Jihar Jigawa - Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da naɗin Zainab Shuaibu Rabo Ringim a matsayin babbar mataimakiyarsa ta musamman kan harkokin yaɗa labarai tare da wasu mataimaka 116.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar (SSG), Mallam Bala Ibrahim, cewar rahoton Leadership.
Wacece Zainab Rabo Ringim?
Zainab, tsohuwar ƴar jarida kuma tsohuwar ma’aikaciyar gidan rediyon Jigawa, wakiliyar gidan rediyon Jamus (Deutsche Welle), kuma tsohuwar mataimakiyar shugabar ƙungiyar mata ƴan jarida ta ƙasa (NAWOJ).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da naɗin nata, Zainab ta zama mace ta farko da aka naɗa a matsayin mai taimaka wa gwamnan jihar Jigawa a fannin yaɗa labarai tun bayan kafa jihar a shekarar 1991.
Sanarwar ta kuma bayyana amincewa da naɗin wasu mataimaka na musamman guda 116 da kuma manyan mataimaka na musamman.
A cewar sanarwar, an yi naɗin ne bisa cancanta, ƙwarewa, da kuma hali na gari.
"Muna da babban aiki a gaban mu, kuma dole ne ku bayar da gudunmawa kan tsare-tsare guda 12 na mai girma Gwamna Umar Namadi, domin gina Jihar Jigawa da muke fata." A cewar SSG.
Gwamna Namadi ya rantsar da kwamishinoni
Gwamnan Umar Namadi ya rantsar da sabbin kwamishinoni 16 da ya naɗa a majalisar zartaswar gwamnatinsa.
Gwamna Namadi ya buƙaci kwamoshinoni su yi aiki bisa tsoron Allah, gaskiya da riƙon amanar al'umma da kuma sauke haƙƙi.
Za a Samar da Miloniyoyi a Jigawa
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi, ya sanar da shirinsa na samar da attajirai a jihar Jigawa.
Gwamna Namadi, ya kaddamar da wani shiri na samar da attajirai 150 a wa’adinsa na farko a ofis.
Asali: Legit.ng