Kungiyar SERAP Za Ta Shigar da Kara Kan Shugaba Tinubu da Gwamna Uzodinma Kan Abu 1
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da gwamnan jihar Imo, Hope Uzodonma sun samu kansu cikin matsala saboda shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa
- Ƙungiyar SERAP ta yi barazanar shigar da ƙara a kansu a gaban kotu saboda lakaɗawa Joe Ajaero duka da aka yi a jihar Imo
- Shugaban na NLC ya ci dukan tsiya ne lokacin da ya yi yunƙurin jagorantar wata zanga-zanga a jihar Imo
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar SERAP ta yi barazanar kai ƙarar Shugaba Bola Tinubu da gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, kan harin da aka kai wa shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), Joe Ajaero.
A makon da ya gabata ne ƴan sanda suka kama Ajaero, gabanin zanga-zangar da aka yi a jihar Imo.
Sai dai rundunar ƴan sandan ta musanta kama Ajaero, inda ta bayyana cewa an tsare shi ne kawai domin kare kai masa hari. Sai dai, Uzodimma ya zargi shugaban ƙungiyar ƙwadagon da yin katsalandan a harkokin siyasar jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa SERAP za ta kai Tinubu da Uzodinma ƙara?
A wani saƙo da ƙungiyar ta sanya a a ranar Talata, 7 ga watan Nuwamba a shafinta na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter), ta yi nuni da cewa za ta shigar da gwamnatin Tinubu da Gwamna Uzodinma ƙara kan abin da aka yi wa Joe Ajaero.
Saƙon na SERAP na cewa:
"Za mu shigar da ƙara kan gwamnatin Tinubu da gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, kan mummunan harin da aka kai wa shugaban NLC na ƙasa, Joe Ajaero, a makon da ya gabata a jihar Imo, da kuma gazawar hukumomi wajen gurfanar da wadanda ake zargi da aikata laifin a gaban kuliya."
Ajaero ya labarta yadda ya ci dukan tsiya
Shugaban ƙungiƴar ƙwadago ta ƙasa, Joe Ajaero, ya bayyana yadda jikinsa ya gaya masa a hannun jami'an tsaro a jihar Imo bayan sun yi awon gaba da shi.
Ajaero ya bayyana cewa Allah ya ƙaddara yana da sauran shan ruwa a gaba, amma dukan da ya sha a hannun jami'an tsaro ya kusa sanya wa ya sheƙa barzahu.
SERAP Ta Kai Karar Tinubu Kotu
A wani labarin kuma, ƙungiyar SERAP ta maka shugaban ƙasa Bola Tinubu ƙara a gaban wata babbar kotun tarayya da ke jihar Legas.
SERAP ta shigar da Tinubu ƙarar ne kan ɓacewar $15bn kuɗaɗen shiga na man getur da N200bn na gyaran matatun man fetur.
Asali: Legit.ng