Kotu Ta Yanke Wa Mutum 6 Hukunci Kan Damfarar Kakakin Majalisa N38m
- Kotu ta aika boka da wasu mutane biyar magarkama saboda hada kai wajen aikata damfara
- Mutanen shida sun damfari tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Osun, Timothy Owoye, tsabar kudi har naira miliyan 38 da yada bidiyon tsaraicinsa
- Mai shari'a Emmanuel Ayoola ya yanke wa kowannensu hukuncin shekaru biyar a gidan yari
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Osun - Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Osogbo ta yanke wa mutum shida ciki harda boka hukuncin shekaru biyar a gidan yari.
Kotu ta yanke masu hukuncin ne kan watsa bidiyon tsaraicin tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Osun, Timothy Owoye, a intanet bayan sun damfare shi naira miliyan 38.
Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, wani bidiyon Timothy Owoeye mai tsawon sakan 13 ya yadu a shekarar 2018 inda aka hano shi yana wanka a cikin wata kasuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi zargin cewa kakakin majalisar ya yi yan tsafe-tsafe ne don dakile mutuwa lokacin da al’ummar yankin Osunjela da ke jihar Osun suka kafa masa kawon zuka.
Yadda kotu ta hukunta boka da wasu 5 kan damfarar miliyan 38
Saboda haka, an gurfanar da masu laifin; Kazeem Agbabiaka, Femi Oyebode, Abdul-Rasheed Ojonla, Babatunde Oluajo, Adebiyi Kehinde, Oyebanji Oyeniyi da Ismaila Azeez a gaban wata kotun majistare kafin aka mika su ga babbar kotun tarayya a ranar 19 ga watan Oktoba, 2018.
Yayin shari'ar, lauyan masu shigar da kara a karkashin jagorancin Moses Faremi ya gabatar da hujjoji guda 57 da suka hada da bayanan bankin da aka tura kudaden damfarar, faifan disc, karamin akwatin katako, dala 100, bindiga da sauransu a gaban kotu.
INEC ta bi Umarnin kotun ɗaukaka ƙara, ta yi gyara a jerin sunayen 'yan takarar Gwamnan jihar Bayelsa
Haka kuma, mutum shida sun bayar da shaidu kan masu laifin ciki harda tsohon kakakin majalisar, Timothy Owoeye, jami'in dan sandan bincike da ma'aikatan banki hudu.
Da yake zartar da hukuncinsa a ranar Talata, 7 ga watan Nuwamba, Mai shari'a Emmanuel Ayoola ya yanke wa mutanen shida kan zargin hada kai, damfara da sauransu.
An yankewa Agbabiaka (boka), Oyebode (shugaban al'umma), Ojonla (shugaban al'umma) da Babatunde (Yarima) hukunci kan hada kai da damfara yayin da aka hukunta Adebiyi huwere kan hari ta yanar gizo.
Sai dai kuma, Mai shari'a Ayoola ya sallami Oyeniyi kan zargin hada kai da masu laifi da aka yi masa.
Mai shari'a Ayoola ya tabbatar da cewa masu laifin sun damfari tsohon kakakin majalisar naira miliyan 38 sannan suka yada bidiyon tsiraicinsa a yanar gizo wanda ya sa aka rika yi wa(Owoeye) ba'a.
Yayin da yake jawabi, lauyan masu laifin ya roki alkalin da ya yi masu sassauci kan cewa sun kasance karo na farko kenan da suke aikata laifi kuma suna da iyali.
Daga bisani Mai shari'a Ayoola ya hukunta dukkan masu laifin zuwa shekaru 5 a gidan yari.
An zargi basarake da yiwa yarinya fyade
A wani labarin, mun ji cewa wani mutum mai suna Ya'u Muhammad, ya zargi hakimin kauyen Dan Gulam da ke karamar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa, Umar Ibrahim, da yiwa diyarsa fyade, tare da kunsa mata ciki sannan ya sa mata cutar kanjamau.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, an yi zargin ne a cikin wata wasika mai kwanan wata 16 ga watan Oktoba 2023 da taken "Sanarwar gurfanar da Umar Ibrahim (Hakimin kauyen DanGulum) kan laifin fyade wanda ya yi karo da sashi 3 (1) (A da D) na dokar VAPP 2021".
Asali: Legit.ng