Kano: NDLEA Ta Cafke Makafi 3 da Ke Safarar Miyagun Kwayoyi, Sun Fadi Yadda Su Ke Jigilar Kwayar
- Hukumar NDLEA ta cafke makafi uku kan zargin safarar miyagun kwayoyi zuwa jihar Kano
- Makafin guda uku da ake zargin su na safarar kwayoyin ne daga Legas zuwa jihar Kano
- Hukumar NDLEA ce ta sanar da kame wadanda ake zargin a hanyarsu ta zuwa Kano daga Legas
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Jami’an Hukumar NDLEA sun cafke wasu makafi guda uku kan zargin safarar miyagun kwayoyi.
Wadanda ake zargin su na safarar kwayoyin ne tsakanin jihar Legas zuwa Kano kafin asirinsu ya tonu, Legit ta tattaro.
Mene NDLEA ke zargin makafin a kai?
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta inda ta ce an kama daya daga cikinsu mai suna Adamu Hassan a Gwagwalada.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce Adamu mai shekaru 40 an same shi da kilo 12 na miyagun kwayoyin a kan hanyarsa ta Kano zuwa Legas a ranar 28 ga watan Oktoba.
Daraktan yada labarai na hukumar, Femi Babafemi shi ya tabbatar da haka a ranar Lahadi 5 ga watan Nuwamba inda ya ce daya makahon ya tsere.
Ta yaya NDLEA ta kama makafin?
Babafemi ya ce Hassan ba shi da masaniyar abin da ke kunshe a cikin kayan da aka ba shi don kai wa jihar Kano.
Ya ce hukumar NDLEA ta kai samame ne bayan samun bayanan sirri na wadannan mutane inda ta yi nasarar kama shugabansu.
Ya ce:
“Bayanan sirri da mu ka samu shi ya ba mu nasarar kama shugaban nasu mai suna Bello Abubakar mai shekaru 45 wanda ya kasance makaho.
“A cikin bayanansa, Bello wanda ya yi aure har da yara biyar ya ce ya na rayuwa a Legas fiye da shekaru 30 amma ya fara harkar kwaya shekaru biyar da su ka wuce.
“Daya daga cikinsu mai suna Muktar Abubakar mai shekaru 59 wanda shi ma makaho ne ya na da yara guda uku wanda su ke rayuwa a Legas.”
Femi ya kara da cewa sun kama na ukun nasu wanda ya kasance matashi mai shekaru 25 mai suna Akilu Amadu wanda shi ma makaho ne.
‘Yan sanda sun kama ‘yan fashi 4 kan kisan dan uwansu
A wani labarin, jami’an ‘yan sanda sun kama ‘yan fashi hudu kan zargin kisan dan uwansu.
Rundunar ta ce ta kama wadanda ake zargin ne bayan sun hallaka dan uwansu saboda ya cinye mu su ganima.
Asali: Legit.ng