Babban Ofishin Jakadancin Ƙasar Waje a Najeriya Ya Kama da Wuta a Abuja, Bayanai Sun Fito

Babban Ofishin Jakadancin Ƙasar Waje a Najeriya Ya Kama da Wuta a Abuja, Bayanai Sun Fito

  • Ana fargabar mutane sun mutu yayin da ofishin jakadancin ƙasar Kanada a Najeriya ya kama da wuta a Abuja
  • Rahotanni sun nuna cewa wutar ta kama ne yayin da ake kokarin gyara wutar lantarkin ofishin, inda ta yi ajalin mutum biyu
  • Duk da babu wata sanarwa a hukumance daga Ofishin amma hukumar kashe gobara ta FCT Abuja ta tabbatar da afkuwar lamarin

FCT Abuja - Wani ɓangaren ginin ofishin jakadancin ƙasar Kanada a Najeriya ya kama da wuta rigi-rigi a babban birnin tarayya Abuja ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba.

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa wasu sassan ofishin jakadancin Kanada wanda ke a lamba 13010G Palm Close, Diplomatic Drive, Central Business District a Abuja ne suka kama ci da wuta.

Hoton yadda wuta ta kama a ofishin.
Babban Ofishin Jakadancin Ƙasar Waje a Najeriya Ya Kama da Wuta a Abuja, Bayanai Sun Fito Hoto: leadership
Asali: UGC

Sai dai har yanzun babu cikakken bayani kan ainihin abin da ya haddasa tashin wannan gobara a babban ofishin jakadancin na ƙasar waje.

Kara karanta wannan

Makinde: Gwamnan PDP ya ciri tuta, ya yi ƙarin albashi mai tsoka ga ma'aikata da 'yan fansho

Amma Hotunan da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna yadda hayaƙi ke fitowa daga ginin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana fargabar rasa rayuka

Jaridar Leadership ta rahoto cewa ana fargabar aƙalla mutum biyu sun mutu yayin da wani ɗaya ya samu raunuka masu muni yayin wutar da ta kama a Ofishin.

A cewar shaidun gani da ido, lamarin ya faru ne a lokacin da ake gyaran wutar lantarkin Ofishin Jakadancin, kwatsam wuta ta kama.

Wannan gobara da ta barke ta yi sanadiyar mutuwar mutane biyu yayin da mutum daya ya samu munanan raunuka, wani kuma ya tsere ta rufin wurin.

Majiyoyin sun ce wadanda abin ya shafa na daga cikin ma’aikatan da ke aikin gyara wutar lantarkin lokacin da ibtila'in ya faru.

Shugaban sashin ayyuka na hukumar kashe gobara ta Abuja, Amiola Adebayo ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an garzaya da wasu da abin ya shafa asibiti.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan Boko Haram sun sake yi wa manoma 9 yankan rago a Borno

Sai dai Adebayo bai bayyana musabbabin tashin gobarar ba ko kuma wadanda abin ya shafa ‘yan kasashen waje ne ko kuma ‘yan Najeriya ne.

Gwamnan PDP Ya Ciri Tuta

A wani rahoton Seyi Makinde ya kara wa ma'aikata N25,000, masu karban fansho N15,000 a matsayin tallafin rage radaɗi na tsawon wata 6.

Gwamnan ya bayyana haka ne a gaban shugabannin ƙungiyoyin.kwadago reshen jihar jihar a bakin shiga Ofishinsa a Ibadan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262