Gwamnan PDP Ya Ciri Tuta, Ya Ƙara Wa Ma'aikata da Ƴan Fansho Albashi a Jiharsa
- Seyi Makinde ya kara wa ma'aikata N25,000, masu karban fansho N15,000 a matsayin tallafin rage radaɗi
- Gwamnan ya bayyana haka ne a gaban shugabannin ƙungiyoyin kwadago reshen jihar jihar a bakin shiga Ofishinsa a Ibadan
- Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya ta ƙara wa ma'aikata N35,000 a albashinsu domin rage radadin cire tallafin mai
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Oyo - Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya amince da biyan N25,000 ga ma'aikata da kuma N15,000 ga masu karbar fansho a matsayin kyautar albashi, The Nation ta ruwaito.
Gwamnan na jam'iyyar PDP ya ce wannan ƙarin albashin zai shafe tsawon watanni 6 kuma sakamakon haka za a samu ƙarin Naira biliyan 2.2 a tsarin albashin Oyo.
Makinde ya yi wannan furuci ne yayin da yake jawabi ga dandazon ma'aikata a ƙofar shiga ofishin gwamna da ke gidan gwamnatin jihar Oyo a Ibadan ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manyan jiga-jigan da suka raka Makinde
Gwamnan ya samu rakiyar shugabannin ƙungiyoyin kwadago na jihar wanda suka haɗa da, Kwamared Kayode Martins (NLC), Kwamarwd Bosun Olabiyi (TUC), da Kwamared Olaonipekun Oluwaseun.
Dukkansu sun halarci wurin da Gwamna Makainde ya ambaci ƙarin tagomashi ga ma'aikata da ƴan fanshon jihar Oyo ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba, 2023.
Sauran kusoshin gwamnati da suka take wa Makinde baya yayin wannan jawabi sun haɗa da mai bada shawara ta musamman kan harkokin kwadago, Adebayo Titilola-Sodo, da Idowu Ogedengbe da sauransu.
Tun da farko, ma'aikatan sun mamaye ofishin mai girma gwamnan a wani ɓangare na matsayar da suka cimma wa zamansu na ranar Litinin.
Sun yi haka ne domin tabbatar da an kawo ƙarshen batun karin albashin lokaci ɗaya duba da wahalar da aka shiga tun bayan cire tallafin man fetur.
Obi ya maida martani ga hukuncin Kotun ƙoli
A wani rahoton kuma Mista Peter Obi ya caccaki hukuncin Kotun ƙoli yana mai cewa ta rusa tunanin ƴan Najeriya na samun adalci a ɓangaren shari'a
Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar LP ya faɗi haka ne yayin hira da ƴan jarida a Abuja ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba, 2023.
Asali: Legit.ng